ABU Zariya: Tarihin Farfesa Kabiru Bala a takaice

ABU Zariya: Tarihin Farfesa Kabiru Bala a takaice

1. Haihuwa

An haifi Farfesa Kabir Bala ne a Ranar 7 ga Watan Junairun 1964 a Garin Kaduna. A lokacin ya na karami, Bala ya yi karatun addini musamman bangaren hadisi har aka rika kiransa Malam.

Farfesa Bala ya taba shaidawa ‘Yan jarida cewa Mahaifinsa ne ya dage wajen ganin sun yi karatun addini da na zamani tun ya na ‘Dan shekara 4. Wannan ya taimake sa sosai a rayuwarsa.

2. Ilmin Boko

A shekarar 1981, Kabir Bala ya kammala Sakandare a Makarantar Barewa ta Zariya. Daga nan ya shiga makarantar sharar fage ta ABU a 1982. A 1985 ya kammala Digiri a ilmin gine-gine a ABU.

Shehin Malamin ya yi Digirinsa na biyu (M.Sc) a sha’anin gine-gine a 1998. A 2001 kuma ya zama Dakta a fanninsa bayan kammala PhD. Bayan haka Bala ya na da Digirin MBA duk a jami’ar.

3. Aiki

Kabir Bala ya soma aiki ne da kamfanin Amana Development Company bayan gama jami’a. A 1987 ya yi dace aka yi masa tayin aiki a jami’ar da ya kammala. A 2007 ya zama Farfesa.

Yayi aiki a matsayin Malamin aro a jami’o’in waje; Abertay, Dundee da ke kasar Scotland a shekarun baya. Sannan ya hada-kai da jami’ar Salford wajen ba ABU Zariya gudumuwa.

4. Karantarwa

Fitaccen Malamin ya koyar da ilmin kimiyyan gini ga masu Digiri da Digirgir har Digir-digir. Kabir Bala ya yaye Dalibai masu Digiri na biyu da na uku kusan 50.

Haka zalika wannan Malami ya yi rubuce-rubuce fiye da 80 a gida da kasar waje. Kabir Bala ya yi mafi yawan rubutunsa ne bayan ya zama Farfesa.

KU KARANTA: Jami'ar ABU Zariya ta nada sabon Shugaba da zai hau kujera a Afrilu

5. Mukamai

Farfesa Bala ya taba rike kujerar shugaban sashensa har sau biyu a Jami’a. Na farko daga 2001 zuwa 2006. Sannan kuma ya sake rike wannan kujera a Farfesansa daga 2010 zuwa 2014.

Bala ne ya fara rike tsangayar ICT na sadarwar zamani na jami’ar ABU a karkashin shugabancin Farfesa S. U Abdullahi. A wannan lokaci kuma ya zama mataimakin shugaban sashe har 2008.

Tsakanin 2010 zuwa 2013, Bala ya rike shugaban kula da tsare-tsaren karatu na ABU Zariya. Daga nan ne Farfesan ya rike makarantar karatun gaba da Digiri kafin ya samu karin matsayi a 2017.

A farkon 2017, aka zabi Kabir Bala a matsayin mataimakin shugaban jami’a. Ya rike wannan kujera na shekaru biyu a lokacin shugaba mai-ci, Ibrahim Garba, kafin a maye gurbinsa.

6. Sauran dawainiya

A 2013, Kabir Bala ya zama shugaban kungiyar CORBON ta Maginan Najeriya. Haka zalika a wannan shekara ya shiga cikin manyan majalisar hukumar NUC mai kula da jami’o’in Najeriya.

Farfesa Bala ya na cikin ‘Ya ‘yan kungiyoyin gida da na kasar waje irinsu NIOB, IFMA ta Amurka, da CABE ta Ingila. Har wa yau ya na cikin ‘Yan kungiyar APM ta kasar Ingila da sauransu.

Shehin Malamin ya halarci taron bita da karawa juna sani bila-adadin a fadin Najeriya da ketare.

7. Shugaban jami’a

A Ranar 22 ga Watan Junairun 2020 aka bada sanarwar cewa Farfesa Kabir Bala ne zai zama sabon shugaban jami’ar ABU Zariya. Zai dare kan wannan kujera ne a karshen Afrilun 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel