Shugaban farko na jam'iar jihar Gombe, Farfesa Abdullahi Mahadi ya rasu.

Shugaban farko na jam'iar jihar Gombe, Farfesa Abdullahi Mahadi ya rasu.

  • Shugaban jami'ar jihar Gombe na farko ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma'a da ta gabata
  • Farfesa Abdullahi Mahadi ya rasu ne yana da shekara 77 a duniya, yayi aiki sosai a jami'o'i da dama a ƙasar nan
  • Gwamnan jihar Gombe ya aiki da saƙon ta'aziyyar sa ga iyalan mamacin da ƙasa gabaɗaya

Shugaban farko na jam'iar jihar Gombe (GSU) dake a Kashere, Farfesa Abdullahi Mahadi, ya rasu, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Mahadi, wanda ya taɓa a lokacin baya shugabantar jami'ar Ahmadu Bello (ABU) dake Zaria, a jihar Kaduna, ya rasu ne a daren ranar Juma'a yana da shekara 77 a duniya.

Abdullahi Mahdi.
Shugaban farko na jam'iar jihar Gombe, Farfesa Abdullahi Mahadi ya rasu Hoto: leadership
Asali: UGC

A halin da ake ciki yanzu, gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya aike da ta'aziyyar sa game da rasuwar Farfesa Mahadi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Darusa 10 da Za a Dauka daga Shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara – Kabir Asgar

Inuwa a wata sanarwa da hadimin sa kan harkokin sadarwa Ismaila Uba Misilli, ya rattaɓawa hannu, ya bayyana mamacin a matsayin wani babban jigo a harkar ilmi, wanda ya gudanar da ayyukan sa cike da kishi da jajircewa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan yayi nuni da cewa ayyukan kwarai da Farfesa Mahadi yayi a jami'ar jihar Gombe da sauran jami'o'in da yayi aiki tarihi ba zai manta da su ba.

Tabbas mun yi rashin muhimmin mutum, shugaba mai nagarta, wanda ya bar tarihi a ɓangaren harkar ilmin mu. Za ayi rashin gogewar sa da ƙwarewar sa a wajen harkar ilmi da kula da muhalli.

Ya buƙaci iyalan mamacin da su ɗauki dangana duba da cewa Farfesan ya gudanar da rayuwa cike da bautar ubangiji da taimakon al'umma, sannan ya tafi ya bar suna mai kyau.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Samu Sabon Sumfurin Shugaba Buhari, Doguwa Ya Jaddada Wanda Ya Dace da Mulki a 2023

Gwamnan a madadin mutanen jihar Gombe, yana miƙa ta'aziyyar sa ga iyalan mamacin, ƴan'uwan sa da abokan aikin sa da ƙasa gabaɗaya, inda yayi addu'ar Allah ya yafe masa kura-kuran sa.
Sannan ya bashi ladan ayyukan sa na ƙwarai da Aljannat Firdaus. A cewar sanarwar.

Tsohon Dan Majalisar Tarayya Daga Jihar Oyo, Nicholas Ojo Alokomaro, Ya Rasu

A wani labarin kuma Allah ya yi wa wani babban Basarake a jihar Oyo kuma tsohon ɗan majalisar tarayya raasuwa

Alakata na Akata da ke Igbomoso ya rasu a ranar Juma'a, 9 ga watan Disamba, bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

Marigayin ya yi aiki a matsayin da majalisar wakilai ta tarayya daga 1992 zuwa 1993 kuma ya wakilci mazabar Ogbomoso ta kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262