Gwamnatin Tinubu Ta Tsaida Lokacin Da Za a Fara Biyan Sabon Tsarin Albashin Ma’aikata
- Gwamnatin tarayya tayi alkawari cewa za ayi watsi da tsarin albashin da ake kai da ‘yan watanni kadan
- Ministan labarai da wayar da kai ya nuna zuwa Afrilu, za a karkare magana kan karin albashin ma’aikata
- Idris Mohammed ya yi bayanin inda aka kwana bayan gwamnatin Najeriya ta janye tsarin tallafin fetur
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce sabon mafi karancin albashi da za a fito da shi zai fara aiki daga 1 ga watan Afrilu 2024 a Najeriya.
Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma, Idris Mohammed ya shaida haka a wata hira da yayi da Punch a birnin tarayya Abuja.
Sabon albashi zai fito a Afrilun 2024
Alhaji Idris Mohammed ya ce tsarin albashin da ke amfani da shi zai daina aiki daga Maris, daga nan mafi karancin albashin zai canza.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya ce tsarin kashe kudi ya nuna gwamnatin tarayya za ta batar da N24.66tr a kan albashi a shekarun 2024, 2025 da kuma 2026.
A sakamakon cire tallafin man fetur, Bola Tinubu ya amince a rika biyan N35, 000 ga ma’aikatan gwamnati kafin ayi ainihin karin albashi.
Matsin lambar kungiyar kwadago ya jawo gwamnati ta na kokarin yadda za a kara mafi karancin albashi daga N30, 000 da ake biya.
Jawabin Minista kan karin albashi
"Shakka babu akwai sabon tsarin albashi da zai fara aiki daga 1 ga watan Afrilu 2024.
Shiyasa aka fara rabon tallafi saboda a rage radadin tattalin arziki. A zamanmu da ‘yan kwadago, an ce karin ba aikin mutum guda ba ne.
Kwamiti da ya ke kunshe da ‘yan kwadago da kan su zai yi aiki kan batun (karin albashin). Ana kafa kwamitin, ana tattaunawa da ma’aikata.
Mu na sa ran sabon tsarin albashi ya fara daga watan Afrilu. A wannan tsari ne za a samu tsayayyen kudin da za a karawa ma’aikata a kasa.
- Mohammed Idris
Wani jami’in NLC ya tabbatar da maganar Idris inda gwamnati ta ke fatan gwamnoni da ‘yan kasuwa za su yi wa ma’aikata karin albashin.
Ana bincike kafin a kara albashi
Ana da labari cewa duk ma'aikacin da ba a iya tantacewa ba, za a cire sunansa daga cikin jeringiyar masu karbar albashi daga Disamban nan.
An dauki tsawon lokaci domin gano ainihin masu aiki, an yi hakan ne domin a huta da biyan albashin bogi a ma'aikatun gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng