Akpabio Ya Bukaci Tinubu Ya Haramtawa Ministocinsa Fita Kasashen Waje, Ya Bayyana Dalili
- Godswill Akpabio, ya roki shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ya sanya dokar hana fita waje na wucin gadi ga ministoci da shugabannin ma'aikatu
- A cewar shugaban majalisar dattawan, sanya dokar zai taimaka wa majalisun tarayya guda biyu kammala kare kasafin kafin karshen watan Disamba
- Ya ce ba ya son abinda ya faru a wajen kare kasafin 2023 ya faru a 2024 inda wasu ministoci da shugabannin ma'aikatu ke bijirewa gayyatar majalisar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja- Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, ya bukaci Tinubu ya sanya dokar hana fita kasashen waje akan ministoci da shugabannin ma'aikatun kasar.
Akpabio ya mika wannan bukatar ne a ranar Laraba a yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 inda ya nemi shugaban ya sanya dokar har zuwa bayan kare kasafin.
Yaushe za a fara kare kasafin 2024?
Shugaban majalisar kai tsaye na son Tinubu ya haramtawa ministoci da shugabannin ma'aikatun fita waje don gudun suki bayyana idan aka zo kare kasafin kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce majalisar dattawa da ta wakilan tarayya za ta bi diddigin kasafin kudin 2024 kafin ta amince da shi har ta sanya hannu, Premium Times ta ruwaito.
A mako mai zuwa ne ake sa ran za a fara kare kasafin kudin 2024, wanda kuma ake sa ran za a kammala kafin karshen watan Disamba.
Mene ya sa majalisa ke son a hana ministoci fita waje?
Akpabio ya ce:
"A karshe ina so in sanar da shugaban kasa cewa za mu tabbatar da cewa kasafin da ka gabatar ya samu kulawa da musamman cikin hadin kai da yakana.
"Da wannan muke fatan shugaban kasa zai sanya dokar hana fita kasashen waje ga ministoci da shugabannin hukumomi har zuwa kammala kare kasafin.
"Idan muka yi la'akari da yadda ta faru wajen kare kasafin 2023, muna fatan za a sa dokar don dakile masu barin kasar da nufin gujewa kare kasafin ma'aikatarsu."
Tun da farko a wani zama da majalisar dattawa ta yi, ta nemi Tinubu ya kori duk wani minista ko shugaban ma'aikata da ya bijirewa gayyatar majalisar don kare kasafin 2024, The Cable ta ruwaito.
A shekaru 24 Najeriya ta kafa tarihin da ya dauki Amurka shekaru 185
A wani labarin, Sanata Akpabio ya ce Najeriya ta kafa wani tarihi da ya dauki kasar Amurka shekaru 185 duk da cewa shekarun Amurka 247 da fara dimokuradiyya, rahoton Legit Hausa.
Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da Tinubu ya gabatar da kasafin naira tiriliyan 27.5 gaban majalisar tarayya
Asali: Legit.ng