Gwamna Adeleke Na Osun Ta Soke Bukukuwan Ranar 'Yancin Kai

Gwamna Adeleke Na Osun Ta Soke Bukukuwan Ranar 'Yancin Kai

  • Gwamna Adeleke na jihar Osun ya soke bikin ranar samun 'yancin kan Najeriya wanda ya saba gudana ranar 1 ga watan Oktoba
  • A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, ya roƙi mazauna jihar da su yi addu'ar Allah ya kawo zaman lafiya a ƙasar nan
  • Adeleke ya taya ɗaukacin 'yan Najeriya murnar zuwan wannan rana, inda ya ce zasu rungumi addu'a domin murnar cika 63

Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ya sanar da soke dukkan bukukuwan murnar ranar samun 'yancin kan Najeriya a faɗin jihar Osun.

Channels tv ta tattaro cewa an shirya gudanar da bikin ne ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, 2023 domin murnar cikar Najeriya shekaru 63 da samun 'yancin kai.

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke.
Gwamna Adeleke Na Osun Ta Soke Bukukuwan Ranar 'Yancin Kai Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

Matakin soke bikin 'yancin kai na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mista Olawale Rasheed, ya fitar a Osogbo, ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Uba Sani: Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Hukuncin da Kotu Zabe Ta Yanke a Jihar Kaduna

Abin da ya kamata yan Najeriya su yi - Adeleke

A sanawan, Gwamna Adeleke ya yi kira ga ɗaukacin al'ummar jihar Osun su yi addu'ar Allah ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton Sahara Reporters, Gwamna Adelele ya ce:

“Mu yi amfani da ranar ‘yancin kai don yin nazari, tunani da kuma yin addu’a kan halin da ƙasar nan ta wayi gari a ciki. Jama'a da dama suna cikin mawuyacin hali.
"Lokaci ya yi da za mu dawo cikin hayyacin mu, mu nemi Ubangiji ya kawo mana ɗauki da kariya a cikin al’amuran tafiyar da ƙasar mu.”
“Ina taya mutanen Osun da ’yan Najeriya gaba daya murna yayin da ranar samun ‘yancin kan ƙasar mu ke ƙwankwasa mana kofa. A nan Osun, za mu yi biki da tunani da addu’a.”

Kara karanta wannan

Jami'an Tsaro Zasu Kama Kwankwaso Kan Barazana Ga Rayuwar Alkalan Kotu? Sabbin Bayanai Sun Fito

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin jihar Kwara ta sanar da cewa ba zata yi shagalin murnar 1 ga watan Oktoba ba duba da halin al'umma ke ciki.

Shin Da Gaske An Sanya Wa Ministar Tinubu Guba? Gaskiya Ta Bayyana

Kuna da labarin Ma'aikatar wuraren tarihi da buɗe ido ta musanta rahoton da ke yawo cewa minista, Lola Ade-John, ta ci guba an kwantar da ita a asibiti.

Mai magana da yawun ma'aikatar ta ce rahoton ba gaskiya bane amma ministar na fama da zazzabin cizon sauro wanda a yanzu ta samu sauƙi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel