Yan Sanda Sun Kama Babban Dan Siyasa, Wasu Kan Damfara Ta Naira Miliyan 607

Yan Sanda Sun Kama Babban Dan Siyasa, Wasu Kan Damfara Ta Naira Miliyan 607

  • Rundunar 'yan sanda ta ce ta samu nasarar kama wani dan takarar gwamna da wasu mutane uku kan zargin satar kudi a manhajar Patricia
  • A shekarar 2022 ne wadanda ake zargin sun yi amfani da fasahar kutse inda suka sace sama da naira miliyan 607 na kamfanin Patricia
  • Kamfanin fasaha na Patricia ya na da manhaja ta hada-hadar kudaden crypto, wanda masu laifin suka yi kutse suka sace kudaden masu hannun jari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Yan sanda sun fara kamo bakin zaren damfarar naira miliyan 607 da aka yi wa kamfanin fasaha na Patricia, bayan da aka kama wani Wilfred Bonse da mutane uku.

Kara karanta wannan

Bidiyon zanga-zangar da ta barke a Kano kan zargin 'yan sanda sun kashe farar hula

Lamarin ya tattara ne kan damfara ta yanar gizo, amfani da kwamfuta ba bisa ka'ida ba, yin amfani da wata fasaha ta karkatar da sama da naira miliyan 200.

Babban sufetan 'yan sanda/Abuja/Damfara
A shekarar 2022 ne kamfanin fasaha na Patricia ya mika koke ga babban sufetan 'yan sanda kan zargin an yi kutse a manhajarsu. Hoto: Nigerian Police
Asali: Twitter

A shekarar 2022 ne kamfanin fasaha na Patricia ya mika koke ga babban sufetan 'yan sanda kan zargin an yi kutse a manhajarsu ta hada-hadar kudaden crypto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kutsen ya jawo asarar dukiyar masu hannun jari a kamfanin, tare da dakatar da ayyukan manhajar don dakile faruwar irin hakan a gaba, rahoton jaridar The Guardian.

Abin da binciken 'yan sanda ya gano kan lamarin

A cewar kakakin 'yan sanda na kasa Olumuyiwa Adejobi a taron manema labarai a Abuja a ranar Juma'a, binciken su ya gano yadda lamarin ya faru.

Ya ce an yi amfani da hadin baki wajen aikata damfarar, tare da amfani da fasahar kutse da lalata tunanin kwakwalwar na'urar kamfanin, jaridar The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Mahaifiyar wani rikakken dan daba ta mika shi hannun yan sanda

Wannan ya ba ba masu laifin damar yin amfani da wata fasaha da karkatar da sama da naira miliyan 607 daga asusun manhajar kamfanin Patricia.

An kama wanda ya dauki nauyin matan da suka yi zanga-zanga zigidir

A wani labarin, rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kama wanda ake zargi da daukar nauyin matan da suka fito zanga-zanga zigidir a jihar Anambra, Legit Hausa ta ruwaito.

Wanda ake zargin, Ozo Jeff Nweke, a cewar rundunar 'yan sanda an kama shi ne a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel