Tsige Abba: Magoya Bayan NNPP Mata Sun Mamaye Hedkwatar Yan Sanda Ta Kano

Tsige Abba: Magoya Bayan NNPP Mata Sun Mamaye Hedkwatar Yan Sanda Ta Kano

  • Magoya bayan jam'iyyar NNPP mata sun mamaye hedkwatar yan sandan jihar Kano kan tsige Abba Kabir Yusuf
  • Ɗaruruwan matan sun yi tattaki tun daga gidan Kwankwaso zuwa babban ofishin yan sanda suna jaddada cewa Abba suka zaɓa a watan Maris
  • Tuni dai NNPP da Abba Gida-Gida suka tunkari kotun ƙoli domin kalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Magoya bayan New Nigeria People's Party (NNPP) sun ci gaba da nuna rashin amincewarsu da hukuncin kotun daukaka kara na tsige gwamna Abba Yusuf na jihar Kano.

Mata sun yi zanga-zanga a Kano.
Tsige Abba: Magoya Bayan NNPP Mata Sun Mamaye Hedkwatar Yan Sanda Ta Kano Hoto: Channelstv
Asali: UGC

A wannan karon mata magoya bayan NNPP ne suka mamaye hedkwatar rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun bayyana kwakkwaran dalilin hana APC da PDP zanga-zanga a Kano

Dandazon magoya bayan NNPP mata sun yi tattaki zuwa hedkwatar ƴan sanda domin nuna adawa da abinda suka kira rashin adalcin kotun ɗaukaka ƙara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da hukumar ƴan sanda ta yi gargaɗi kan fitowa zanga-zanga, ɗaruruwan matan sanye da jajayen hijabai sun fito ɗauke da kwalaye da rubutu daban-daban.

Sun yi tattaki tun daga gidan ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, zuwa hedkwatar ƴan sanda ta Kano ranar Lahadi.

Matan sun yi ta nanata kiran a yi adalci, inda aka ji suna jaddada cewa Abba Kabir Yusuf ne ya lashe zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Wasu daga cikin magoya bayan NNPP sun dage yin tarukan addu'o'i da rokon Allah ya bai wa Abba Gida-Gida nasara yayin da suke ci gaba da zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi garkuwa da shugaban APC a jihar arewa

Abba ya tafi kotun koli

Idan baku manta ba, kotun ɗaukaka ƙara ta yanke cewa tsaida Abba Gida-Gida takara a inuwar NNPP ya saɓawa kundin dokokin zaɓe saboda bai cancanci shiga zaɓe ba.

Saboda haka kotun ta ayyana ɗan takarar APC, Dakta Nasiru Gawuna, a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano.

Amma tuni NNPP da Gwamna Abba suka yi watsi da wannan hukunci, inda suka nufi kotun kolin Najeriya domin ƙalubalantar matakin kotun ɗaukaka ƙara.

Gwamna Yusuf, wanda ya lallasa jam'iyyar APC mai mulki a jihar lokacin zaɓen, ya bayyana hukuncin a matsayin "rashin adalci."

Manyan Jiga-Jigan NNPP Sun Shiga Sabuwar Matsala

A wani rahoton na daban Jam'iyyar NNPP mai alamar kwandon kayan marmari ta yi zargin cewa yan bindiga sun yi barazanar kai hari babbar sakatariyar NNPP.

A wata wasiƙa da jam'iyyar ta tura zuwa ofishin Sufetan yan sanda na ƙasa (IGP) ta ce mutanen sun yi barazana raba wasu kusoshin NNPP da duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel