Yan Banga Biyu 2 Sun Rasu A Artabu Da Yan Bindiga Abuja

Yan Banga Biyu 2 Sun Rasu A Artabu Da Yan Bindiga Abuja

  • Yan ta'adda sun kashe wasu yan banga guda biyu yayin da suka jikkata guda hudu bayan sunyi musu kantar bauna a Abuja
  • Yan bangan sun gamu da ajalin su ne yayin da suka shiga daji ceto wasu manoma da yan bindiga suka sace a gonar su
  • Wani Dan Banga ya ce a yan bindiga sun tsananta kai hare-hare a garuruwan da ke yankin Abaji dake Abuja

Yan ta'adda sun kashe wasu yan banga guda biyu yayin da suka jikkata guda hudu bayan sunyi musayar wuta da junan su a Abuja. Rahoton Aminiya

Yan bangar sun gamu da karshen su ne a lokacin da yan bindigar suka yi musu kwantar bauna a unguwar Gaskpa dake karamar Hukumar Abaji

Wani daga cikin yan bangar da ya tsallake rijiya da baya, Mai suna Ishaku, ya ce harin ya faru ne a wani daji da ke tsakanin Abuja da jihar Neja a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yan Bindige Sun Yi Wa Yan Bijilante Kwanton Bauna, Sun Bindige 2 Har Lahira A Abuja

Ishaku ya bayyana cewa yan bindiga sun kai musu hari ne a lokacin da suke kan hanyar su na ceto wasu manoma da yan bindigan suka sace su a cikin gonar su.

vigilante
Yan Banga Biyu 2 Sun Rasu A Artabu Da Yan Bindiga Abuja FOTO Legit.NG
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ishaku ya ce suna dab da isa mafakar yan bindigar ne kafin suk yi musu kwanton bauna inda suka yi musayar wuta.

Ya ce an dauko gawar mutum biyun da suka rasu, hudun da suka jikkata kuma an kai su asibiti a Jihar Neja.

Wani Dan Banga ya ce yan bindiga sun tsananta kai hare-hare a garuruwan da ke yankin Abaji dake Abuja

Kakakin ’yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, yaki amsa wayar sa a lokacin da aka kira shi domin ji ta bakin shi abun da ya sani game da lamarin.

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Kukan Yadda Ake Kashe Namun Daje Dake Harabar Gidan

Kara karanta wannan

Wasu Mutum Uku Sun Tsallake Rijiya da Baya a Hannun Mutane Bayan Asirin Su Ya Tonu a Abuja

A wani labari kuma Abuja - Mahukuntar fadar shugaban kasa sun bayyana damuwarsu kan kisan da aka yi wa namun daji dake dajin fadar shugaban kasa da ke Abuja. Rahoton Sunnewsonline

Sakataren dindindin na gidan gwamnati, Tijjani Umar, ya yi magana a karshen mako yayin da yake karbar tawagar masu kula da gandun daji na kasa, da takwarorinsu a fadar shugaban kasa, wadda aka fi sani da ‘Royal Rangers’.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel