Ministan Shugaba Tinubu Ya Kai Ziyara Ta Musamman Wajen Buhari a Garin Daura
- Ahmed Aminu Dangiwa ya kai gaisuwa wajen tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a mahaifarsa
- Ministan harkokin gidan ya na cikin mutanen da aka yi tafiyar APP, ANPP da CPC har zuwa APC da su a jihar Katsina
- Muhammadu Buhari ya fara ba Dangiwa kafin Bola Tinubu ya nada shi a cikin Ministocin tarayya a shekarar nan
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Katsina - Ahmed Musa Dangiwa ya kai ziyara zuwa garin Daura a jihar Katsina inda ya yi wani zama da Muhammadu Buhari.
Bayanan da mu ka samu a shafin Ministan da ke dandalin Twitter ya nuna an yi zaman ne a gidan tsohon shugaban kasar.
M. S Ingawa wanda ya na cikin mutanen Mai girma Ministan, ya ce alakar Ahmed Aminu Dangiwa ta fara tun daga shekarar 2002.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashin yake cewa Dangiwa ya na cikin wadanda su ka fara amsa kiran Muhammadu Buhari lokacin da ya shiga siyasa.
Injiniya Ingawa ya ce Ministan harkokin gidajen ya halarci taron masoya da na cikin gida da Buhari ya kira, ya bada gudumuwar N500, 000.
A wancan lokaci kamar yadda Ingawa ya bayyana a shafinsa, Buhari ya nunawa Dangiwa yana so su shigo tafiyar siyasar da za ayi.
Mukaman da Dangiwa ya rike a APC
Bayan shekaru ana gwagwarmaya, Dangiwa ya shugaban jam’iyyar APC na reshen Katsina, ya jagorance ta ga nasara a zaben 2015.
A zaben 2023, shi ne Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Dikko a Katsina inda jam’iyyarsu ta APC ta lashe takarar.
Da Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa, sai ya nada Arch. Dangiwa ya zama shugaban hukumar gina gidaje ta kasa a 2017.
Ana da labari ya nemi tikitin zama Gwamnan Katsina amma bai yi nasara ba, daga baya Dikko Radda ya ba shi sakataren gwamnatinsa.
Shari'o'in zabe sun jawo surutu
Rahoto ya zo cewa tsohon shugaban Lauyoyi, Olumide Akpata yana so kotun daukaka kara ta yi bayani a kan hukuncin zaben gwamnan jihar Kano.
Olumide Akpata ya ce an yi abin kunya don haka yana da muhimmanci Monica Dongban-Mensem ta yi karin haske kan hukuncin da aka zartar.
Asali: Legit.ng