Dangiwa ya gama aikin da Buhari ya ba shi a FMBN, zai yi takarar Gwamna a Katsina

Dangiwa ya gama aikin da Buhari ya ba shi a FMBN, zai yi takarar Gwamna a Katsina

  • Ahmed Musa Dangiwa ya kammala wa'adinsa a matsayin shugaban bankin nan na FMBN a Najeriya
  • Bayan shekara biyar a ofis, Arch. Ahmed Musa Dangiwa ya mika ragamar bankin ga Kabiru Adeniyi
  • Ana tunanin ‘dan siyasar zai nemi takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC a zaben badi

Abuja - Shugaban bankin FMBN mai taimakawa ma’aikata da hanyar mallakar gida a Najeriya, Ahmed Musa Dangiwa ya sauka daga kan kujerar da yake kai.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Ahmed Dangiwa ya bada wannan sanarwa ne a shafinsa na Twitter (@Arch_Dangiwa) a ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu 2022.

Kamar yadda Arch. Ahmed Dangiwa ya bayyana, ya damka ragamar shugabancin bankin kasar ga Mista Kabir Adeniyi a matsayin shugaba na rikon kwarya.

Kara karanta wannan

2023: Amaechi ya fara neman shawarwari, ya ziyarci sarakunan Daura, Kano da Bichi

Kabir Adeniyi zai jagoranci FMBN har zuwa lokacin da shugaban kasa zai nada cikakken shugaba. Wa'adinsa ya zo karshe ne a karshen makon da ya wuce.

Dangiwa ya godewa shugabanni da daukacin ma’aikatan wannan banki da irin gudumuwar da suka ba shi, har ya iya cin ma nasarorin da aka samu a lokacinsa.

A bayanin ban-kwanan da ya yi, Arch. Dangiwa ya ce ya yi alfahari da wannan mukami da ya rike.

Arch. Dangiwa
Arch. Ahmed Musa Dangiwa Hoto: @Arch_Dangiwa
Asali: Twitter

Nasarorin Dangiwa a FMBN

Daga cikin nasarorin da aka rahoto Dangiwa ya samu shi ne bada aron kudi har Naira biliyan 175 da ya yi ga ‘yan Najeriya domin su mallaki gidan kan su.

Haka zalika Arch. Dangiwa ya na alfahari da cewa a lokacin da yake rike da FMBN tsakanin 2017 da 2022 aka samu karin Naira biliyan 294 a asusun bankin.

Kara karanta wannan

Abin da ‘Yan Facebook, Twitter ke ta fada kan shirin takarar Osinbajo a zabe mai zuwa

Takara a jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta na da labari cewa tsohon shugaban bankin na FMBN ya na da niyyar samun takara a APC domin ya gaji Aminu Bello Masari a Katsina.

Mun yi hira da Tameem Karankaki, daya daga cikin matasan da ke tare da Dangiwa, ya kuma shaida mana cewa ‘dan siyasar zai kaddamar da shirin takara.

Malam Tameem Karankaki ya ce nan da wani lokaci za a ji tsohon shugaban bankin na FMBN ya saye fam, kuma su na sa ran jam’iyyar APC ta tsaida shi a 2023.

Karankaki mai jagorantar kungiyar yakin neman zaben Dangiwa ta Dangiwa Frontiers a yankin Funtua ya shaida mana cewa su na ganin lallai za su kai labari.

Rabon kayan azumi

A daidai wannan lokaci ne The Nation ta rahoto cewa Dangiwa ya kashe N91m wajen rabawa shugabannin APC na jihar Katsina kudi da kayan Ramadan.

Kara karanta wannan

Zan daura daga inda Buhari ya tsaya: Alkawura 10 na Osinbajo idan ya zama shugaba a 2023

Hadimin gwamnan Katsina kuma Darekta Janar na yakin neman zaben Dangiwa a 2023, Yahaya Abubakar Kusada ya yi jawabi a wajen rabon kayan azumin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel