Bashin Naira Tiriliyan 87: SERAP Ta Bukaci Bankin Duniya Ya Daina Ba Jihohin Najeriya Bashi

Bashin Naira Tiriliyan 87: SERAP Ta Bukaci Bankin Duniya Ya Daina Ba Jihohin Najeriya Bashi

  • Kungiyar SERAP ta bukaci Bankin Duniya da ya dakatar da ba jihohin Najeriya rancen kudi kan zargin almubazzaranci
  • Kungiyar ta ce babu abin da jihohin kasar ke yi sai aukin karbar bashi amma babu wani aikin azo a gani da ake yi da kudaden
  • Rahoton da SERAP ta fitar ya nuna ana bin jihohi bashin naira tiriliyan 9.17 yayin da ake bin gwantin tarayya bashin naira tiriliyan 78.2

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - Kungiyar kare hakkokin tattalin arziki da bin diddigin ayyuka (SERAP) ta roki Bankin Duniya da ya dakatar da ba jihohin Najeriya rancen kudi.

A cewar SERAP, ta na zargin jihohi 36 na Najeriya da almubazzarancin kudaden jama'a, wanda zai iya hadawa da kudaden da suke karba daga bankin.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kano, Bello, ya bayyana abu 1 tak da ke sa shi farin ciki a rayuwarsa

SERAP/Gwamnonin Jihohi/Bankin Duniya
Bashin da ake bin jihohi 36 hadi da babban birnin tarayya ya kai naira tiriliyan 9.17, yayin da ake bin gwamnatin tarayya bashin naira tiriliyan 78.2. Hoto: @SERAPNigeria
Asali: Twitter

A wata wasika mai kwanan wata 25 ga watan Nuwamba 2023, kungiyar ta nemi shugaban bankin, Ajay Banga, ya gudanar da bincike kan basussukan da aka ba jihohin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohi su yi bayanin yadda suka kashe kudaden da WB ya ba su - SERAP

Kungiyar ta ce idan har an samu johohin da aikata laifin almundahana da almubazzaranci, to bankin ya hana johohin rancen kudi kwata-kwata, Channels TV ta ruwaito.

Ta kuma bukaci bankin ya dakatar da bayar da damar karbar bashi ga jihohi 36 har sai jihohin sun yi bayanin yadda suka kashe kudaden da suke karba daga bankin.

Vanguard ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya fitar a ranar Lahadi.

Adadin kudaden da ake bin jihohi da gwamnatin tarayya bashi - SERAP

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya yabawa Uba Sani kan 'inganta walwalar' mazauna Kaduna

A cewar sanarwar:

"Bai kamata babban bankin da abokan huldarsa su ci gaba da ba jihohin rance kudi ba, akwai zarge-zargen almundahana da almubazzaranci a kansu.
"Mun damu sosai kan zargin jihohin na wadaka da kudaden da suke karba daga bankin ba tare da yin aikin komai ba, bai kamata a kara basu wasu kudin ba."

SERAP ta yi nuni da cewa bashin da ake bin jihohi 36 hadi da babban birnin tarayya ya kai naira tiriliyan 9.17, yayin da ake bin gwamnatin tarayya bashin naira tiriliyan 78.2.

SERAP ta maka Akpabio, Abbas a kotu kan naira biliyan 110 na motocin alfarma

A wani labarin, Kungiyar SERAP ta maka shugabannin majalisun Tarayya, Godswill Akpabio da Tajudden Abbas kan kashe Naira biliyan 110, Legit Hausa ta ruwaito.

Majalisun sun ware Naira biliyan 40 na motocin alfarma da biliyan 70 na tallafi ga sabbin mambobinsu

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.