Yanzu-Yanzu: SERAP Ta Yi Ƙarar Buhari a Kotun ECOWAS, Ta Ɗauki Hayan Femi Falana

Yanzu-Yanzu: SERAP Ta Yi Ƙarar Buhari a Kotun ECOWAS, Ta Ɗauki Hayan Femi Falana

- Kungiyar SERAP da wasu kungiyoyi sunyi karar gwamnatin Shugaba Buhari a kotun ECOWAS

- SERAP da sauran kungiyoyin sun shigar da karar ne ta hannun lauyansu Femi Falana SAN

- A karar, SERAP na son a dage dakatarwa da gwamnatin Buhari ta yi wa Twitter wanda ta ce ya saba wa ka'ida

Kungiyar SERAP mai rajin yaki da cin hanci da tabbatar da mulkin gaskiya a Nigeria da wasu kungiyoyi yan Nigeria 176 sun yi karar Shugaba Muhammadu Buhari a kotun Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, kan haramta wa kamfanin Twitter ayyukansa a Nigeria, The Punch ta ruwaito.

Babban lauya kuma mai rajin kare hakkin bil-adama, Femi Falana, SAN, ne ya shigar da karar mai lamba ECW/CCJ/APP/23/21 a ranar Talata kamar yadda This Day ta ruwaito.

Yanzu-Yanzu: SERAP Ta Maka Buhari a Kotun ECOWAS Kan Haramta Twitter
Yanzu-Yanzu: SERAP Ta Maka Buhari a Kotun ECOWAS Kan Haramta Twitter
Asali: Original

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Wani Mutum Ya Shararawa Shugaban Faransa Emmanuel Macron Mari

SERAP ta ce gwamnatin Nigeria ta dakatar da Twitter ne domin barazana da hana "yan Nigeria amfani da dandalin da sauran dandalin sada zumunta wurin bibiyar tsare-tsare da ayyukan gwamnati ta tona asirin masu rashaawa da wuce gona da iri da jami'an gwamnatin tarayya ke yi."

A cikin takardar karar, SERAP da sauran kungiyoyin suna neman kotun da bada umurnin hana gwamnatin tarayyar Nigeria cigaba da dakatar da ayyukan Twitter a Nigeria ko hana kafafen watsa labarai yin amfani da Twitter, barazana, kamawa ko gurfanar da duk wani mai amfani da Twitter har sai an saurari karar an yanke hukunci.

Wadanda suka yi karar sun ce idan ba a amince da bukatarsu cikin gaggawa ba, gwamnatin tarayyar Nigeria za ta cigaba da dakatar da Twitter ta kuma barazanar gurfanar da yan Nigeria da kamfanonin sadarwa da gidajen watsa labarai da mutane masu amfani da Twitter.

KU KARANTA: Hotunan Dakarun NSCDC Mata Zalla Da Ya Ɗauki Hankulan Mutane a Dandalin Sada Zumunta

A makon da ta gabata ne gwamnatin Shugaba Buhari ta dakatar da Twitter a kasar kan zargin cewa ana amfani da kafar wurin 'tada rikici a kasar ta hanyar raba kan yan kasa.'

Tun bayan zartar da wannan dakatarwar, wasu kasashen ketare kamar Amurka, Canada, Burtaniya da wasu kungiyoyi sunyi ta sukar matakin suna cewa hana yan kasa bayyana ra'ayoyinsu ne.

A wani rahoton daban kun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dauki sabbin ma'aikata 10,000 a ma'aikatu da hukumomin jihar a yayin da ta ke rage yawan ma'aikata a wasu hukumomin, rahoton The Cable.

Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamna Nasir El-Rufai kan watsa labarai ne ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin.

Adekeye ya ce za a dauki ma'aikatan ne cikin wadanda aka tantance yayin aikin daukan sabbin ma'aikata a jihar kamar yadda Sun News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel