Matasa Na Murna Bayan N-Power Sun Fitar da Sabuwar Sanarwa Kan Biyan Basukan Watanni 9

Matasa Na Murna Bayan N-Power Sun Fitar da Sabuwar Sanarwa Kan Biyan Basukan Watanni 9

  • Gwamnatin Tarayya ta bai wa masu cin gajiyar N-Power hakuri kan basukan da su ke bi na tsawon watanni tara
  • Matsana da ke bin bashin mafi yawanci 'yan rukunin 'C' ne da aka dauka a shekarar 2021 inda wasu kebin bashin watanni tara
  • Minista Beta Edu da manajan N-Power, Akindele Egbuwalo sun ba da tabbacin cewa su na kan kokarin biyan kudaden

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An bukaci masu cin gajiyar N-Power da su ke bin bashi su kara hakuri kan basukansu, Legit ta tattaro.

Wadanda ke bin bashin mafi yawanci 'yan rukunin 'C' ne da aka dauka a shekarar 2021 inda wasu ke bin bashi har na tsawon watanni tara.

Kara karanta wannan

Yadda faston da ke sayar da tikitin shiga aljanna ya gusar da hankulan yayanmu, ya raba mu

N-Power ta sha alwashin biyan basukan masu cin gajiyar shirin nan ba da jimawa ba
N-Power ta yi martani kan basukan matasa masu cin gajiyar shirin. Hoto: Dr. Betta Edu.
Asali: Facebook

Yaushe aka dauki matasan a shirin N-Power?

A cikin wata sanarwa da N-Power su a fitar a shafin Twitter, sun sha alwashin kawo karshen dukkan matsalolin da ake fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministar Jin Kai da Walwala Bette Edu da manajan N-Power, Akindele Egbuwalo sun tabbatar da cewa su na kokarin ganin an warware wannan matsalar ta bashi.

Sanarwar ta ce:

"Ku sani cewa mai girma Minista da kuma manajan N-Power yanzu haka su na kokarin ganin sun biya dukkan basukan da ake bi.
"Mu na kara ba ku hakuri, mun gode sosai da irin juriyar da ku ke nunawa."

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari shi ya kirkiri wannan shiri a shekarar 2016 don samar da ayyukan yi ga matasa.

Yaushe aka soke shirin N-Power?

An dauki dubban matasa a bangarorin noma da koyarwa da kuma bangaren lafiya wanda ake biyansu dubu 30 duk wata a matsayin alawus.

Kara karanta wannan

Dandazon mata fiye da 1,000 sun fito zanga-zanga zigidir a Anambra

Rukunin farko na 'A' da aka dauki matasa dubu 200 sun fara aiki ne a 2016 yayin da rukunin 'B' mutum dubu 300 su ka fara aiki a shekarar 2018.

Dukkan rukunan A da B an dakatar da su a shekarar 2020 yayin da aka sake daukar rukunin 'C' a 2021 kafin Tinubu ya soke shirin a watan Oktoban 2023.

Tinubu ya dakatar da shirin N-Power

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da dakatar da shirin N-Power da tsohon shugaban kasa, Buhari ya kirkiro.

Minista Beta Edu ta ma'aikatar jin kai da walwala ita ta bayyana haka inda ta ce su na binciken badakala a shirin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel