Tinubu Ya Fadi Bangare 1 Tak da Yafi Bai Wa Muhimmanci a Gwamnatinsa, Ya Ba da Shawara

Tinubu Ya Fadi Bangare 1 Tak da Yafi Bai Wa Muhimmanci a Gwamnatinsa, Ya Ba da Shawara

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana bangaren da ya shi bai wa muhimmanci a gwamnatinsa yayin wani taro a jihar Ogun
  • Tinubu ya bayyana cewa masarautun gargajiya su ne mafi muhimmanci da zai fi bai wa kulawa wurin ganin ya inganta su a kasar
  • Shugaban, wanda mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilta ya bukaci 'yan kasar su ci gaba da karfafa zaman lafiya da hadin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa masarautun gargajiya sun fi komai muhimmanci a gwamnatinsa.

Tinubu ya bayyana haka yayin murnar bikin Akesan karo na 37 da aka gudanar a karamar hukumar Ikenne da ke jihar Ogun, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya fadi gwaggwabar kyauta ga wadanda su ka lashe musabaka, Bala Lau ya yi martani

Tinubu ya fadi bangaren da ya fi bai wa muhimmanci a gwamnatinsa
Tinubu ya ce masarautun gargajiya su fi komai muhimmanci a wurinshu. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Mene Tinubu ke cewa kan masarautun gargajiya?

Shugaban wanda ya samu waklicin mataimakinsa, Kashim Shettima ya ce inganta masarautun gargajiya shi ne babban abin da Tinubu ya fi bai wa muhimmanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya bayyana jin dadinsa yadda masarautun gargajiya ke taka muhimmiyar rawa wurin inganta al'adun al'umma.

Ya ce bambance-bambancen da ke tsakanin al'ummar kasar shi ke kara musu karfi a matsayin ƙasa guda daya, cewar Daily Post.

Ya shawarci al'ummar Najeriya da su ci gaba da amfani da kuma ribatar darussan da su ka koya a al'adun kasar.

Wace shawara Tinubu ya bayar?

Ya ce:

"Duk da ban yi tsammanin kasa da haka ba, ina amfani da wannan dama wurin godewa Gwamna Abiodun na jihar Ogun da gayyatar mu zuwa wannan biki.
"Ina kuma godewa Oba Adeleke Idowu na Iperu Remo da irin wannan karimci da su ka mana.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi umurnin nada mataimakin Akeredolu a matsayin mukaddashin gwamna? Gaskiya ta bayyana

"Wannan biki zai kara mana kaimi ganin cewa babban abin da Shugaba Tinubu ya fi bai wa muhimmanci shi ne inganta masarautun gargajiya."

Shettima ya kuma shawarci 'yan Najeriya da su ci gaba da karfafa hadin kai da zaman lafiya a kasar, cewar News Now.

Amaechi ya magantu kan tura sunan Wike Minista

A wani labarin, Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana irin kuskuren da ya tafka bayan tura sunan Nyesom Wike a matsayin minista.

Amaechi ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyon da ya karade kafofin sadarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel