Yan bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari a Arewa, Sun Tafka Barna Tare da Kashe Bayin Allah

Yan bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari a Arewa, Sun Tafka Barna Tare da Kashe Bayin Allah

  • Yan bindiga sun kai sabon mummunan hari garin Kaura Namoda da ke jihar Zamfara ranar Talata da daddare
  • Rahoto daga mazauna garin ya nuna cewa maharan sun kashe mutane uku ciki har da mace ɗaya da ɗalibin sakandire
  • Har yanzu hukumar yan sanda ba ta ce komai kan sabon harin ba amma hadimin Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar da faruwar lamarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Mutum uku sun rasa rayukansu ranar Talata da daddare yayin da wasu yan bindiga daɗi suka kai sabon farmaki a garin Ƙaura Namoda da ke jihar Zamfara.

Yan bindiga sun kai sabon hari a Zamfara.
Mutum uku sun rasu yayin da yan bindiga suka kai sabon hari a jihar Zamfara Hoto: premiumtimes
Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa waɗanda maharan suka raba da rayuwarsu a harin sune, Garzali Kaura, Na’ima da ɗalibin sakandire Halifa Dan Tsoho.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Ɗaya daga cikin ɗalibai mata na jami'ar tarayya da yan bindiga suka sace ta kuɓuta

Har yanzu hukumar yan sanda reshen jihar ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan sabon harin ƴan bindigan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma babban mai taimaka wa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara kan harkokin jama'a, Mustapha Jafaru, ya tabbatar da lamarin.

Yadda maharan suka shiga garin da daddare

Wani mazaunin Kaura, Abdulmalik Mohammed, ya ce maharan sun shiga garin cikin garin da misalin karfe 9:00 na dare, kuma kai tsaye suka nufi Kofar Zurmi.

Mutumin ya ce:

"Abun da mamaki saboda yan ta'addan sun shiga mintuna kaɗan bayan karfe 9:00 na dare kuma daga zuwa suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, mutane suka fara gudu."
"Matar da aka kashe tana gudu daga Islamiyya da nufin komawa gida suka bindige ta har lahira. Bayan ita sun kuma harbe wani yaro da ke kokarin shiga gida."

Kara karanta wannan

An kai farmaki hedikwatar rundunar yan sandan jihar Adamawa, bayanai sun fito

Ɗayan wanda aka kashe, Garzali Kaura, wanda mutumin yace ya masa farin sani, shi ma an tsinci gawarsa da harsashi a jikinsa da safe (Laraba).

Jami'an tsaro sun kai ɗauki

Ya ƙara da cewa ba don ɗauƙin gaggawa da jami'an tsaro da yan banga suka kawo ba, da harin ya fi haka muni.

"Ina mamakin yadda maharan na suke tsallake jami'an tsaro daban-daban har suka kawo hari, ban san meyasa sai mun kira sojoji ba, sun yi bakin kokarinsu wajen korar ƴan ta'addan."

Dakarun Sojoji Sun Buɗe Wa Tawagar 'Yan bindiga Wuta

A wani rahoton na daban Sojojin rundunar OPSH sun halaka yan bindiga bakwai a ƙaramar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Oya James, ya ce sojojin sun kwato muggan makamai daga hannun yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel