“Bana Iya Ajiye Ko Kwabo Yanzu”: Dan Najeriya Da Ke Karbar 200k Duk Wata Ya Koka da Tsadar Rayuwa

“Bana Iya Ajiye Ko Kwabo Yanzu”: Dan Najeriya Da Ke Karbar 200k Duk Wata Ya Koka da Tsadar Rayuwa

  • Wani matashi dan Najeriya wanda ke fadi tashi yayin da ake fama da tsadar rayuwa ya ba da labarinsa
  • Khalidu ya zanta da jaridar Legit game da yadda yake tafiyar da abun da yake samu, yana neman karin kudaden shiga, da tallafawa danginsa
  • Yana fatan gwamnati za ta dauki matakin gaggawa don magance halin da tattalin arziki ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Najeriya na fuskantar matsananciyar matsala ta tattalin arziki, inda tsadar farashin kayayyaki ya kai kololuwa a tarihinta a 2023.

Tsadar rayuwa dai ta yi sanadiyyar durkusar da karfin siyayyar yan Najeriya da dama musamman matasa da masu karbar albashi.

Masu karbar 200k duk wata ma basu jinta da dadi
“Bana Iya Ajiye Ko Kwabo Yanzu”: Dan Najeriya Da Ke Karbar 200k Duk Wata Ya Koka da Tsadar Rayuwa Hoto: Getty Images
Asali: TikTok

Daya daga cikinsu shine Sada Khalidu, matashi mai shekaru 29 wanda ke aiki a bangaren kasuwanci a wani kamfanin watsa labarai mai zaman kansa a Kano, birni mafi girma na biyu a kasar.

Kara karanta wannan

"204k kullun, N6.1m duk wata": Dan Najeriya da ke jinyar wani tsoho ya bayyana abun da yake samu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yana karbar albashi N200,000 duk wata, amma ya ce baya isarsa gudanar da abubuwan bukatarsa.

Shi kadai yake rayuwa a wani daki da yake haya kuma yana fatan yin aure nan ba da jimawa ba, amma watakila halin da ake ciki yanzu yana iya sanya shi dage wannan daddaden buri nasa.

Ya fada ma jaridar Legit cewa:

"Tsadar rayuwa ta rage karfin siyayya na matuka, wanda ya sa ina fuskantar kalubale wajen gudanar da yanayin rayuwata ta baya. Yanzu sai na zauna na tsara kudin abinci da ya yi tsada, kudin abun hawa da na bukatun yau da kullun, da kuma bayar da fifiko kan abun da nake bukata bisa ga wanda nake so."

Khalidu ya bayyana cewa cire tallafin man fetur, wanda gwamnatin Shugaban kasa Tinubu ta yi a 2023 ya kara tsadar abun da yake kashewa a kullun kan abun hawa.

Kara karanta wannan

Wike ya magantu kan yiwuwar karawa da Tinubu a zaben 2027

"Da ina kashe N800 kullun kan abun hawa, amma yanzu ina kashe N1500. Ya karu da kaso 90 cikin dari. Hakan na nufin na samu raguwa a kudaden da zan kashe kan sauran abubuwa," inji shi.

Ya kuma bayyana cewa baya iya ajiye komai daga albashinsa saboda farashin chanji, wanda yasa naira ya rasa darajarsa da sama da kaso 20 cikin dari kan dala a watannin da suka gabata.

"A da na kan ajiye tsakanin N30,000 da N50,000 duk wata, amma yanzu bana iya ajiye ko kwabo. Naira na rasa darajarsa a kullun, kuma komai na kara tsada," inji shi.

Khalidu yana shirin nemo karin hanyoyin samun kudaden shiga saboda rashin tabbass wanda ke kara tabarbarar da halin da ake ciki.

"Ina neman karin aiki don samun karin kudin shiga. Na iya aikin zane da daukar hoto, don haka ina kokarin tallata kaina a yanar gizo don samnun wasu abokan ciniki. Amma kun sani wannan abubuwan ba ma su sauki bane."

Kara karanta wannan

Miji ya zargi surukinsa hakimi, basarake a Kano da kashe masa aure tare da yunkurin tozarta shi

A halin yanzu, Khalidu ya ce yana sake tsara aikin kashin kansa da aikinsa daidai da kudaden shigarsa sannan yana neman hanyoyin samun karin kudade don tallafawa danginsa, wadanda suka dogara da shi a wannan lokaci.

“A yanzu haka ina tallafa musu ta kowace irin hanya da zan iya amma neman taimako ya karu daga iyalina fiye da kowane lokaci. Hakika kowa abin ya shafa,” Khalidu ya sake nanata.

Har ila yau, yana fama da matsalolin tunani da tarin gajiya da ke fitowa daga halin da yake ciki a yanzu.

Legit Hausa ta zanta da wasu ma’aikata don jin yadda rayuwa take a bangarensu a yanzu inda duk suka koka da tsadar rayuwa.

Wani magidanci mai suna Malam Anas wanda malamin makaranta ne ya ce yanzu babu abun da za su ce sai neman taimakon ubangiji. Ya ce:

“A matsayina na malamin makarantar sakandare, dududu albshina bai dubu saba’in ne a wata, wallahi baya iya kaini ko’ina saboda ga iyali. Wasu lokutan ma kafin ayi albashin mutum ya tara basussuka ga shi kullun idan za ka shiga kasuwa sai ka samu farashin abubuwa sun sauya. Allah dai ya kawo mana dauki don ba’a taba shiga yanayi irin wannan ba.

Kara karanta wannan

Yadda mai tallar gyada ta zama miloniya, bidiyon sauyawarta ya girgiza intanet

A bangaren Malam Abubakar da ke aiki a wani kamfani ya ce:

“Tabbass ko masu kudi sun san ana cikin wani hali a yanzu. A baya na kan siya duk wasu abubuwan bukatuna a wata harma na samu dan raran kudi da zan ajiye saboda koda wani abu zai taso. Sai dai fa yanzu babu wannan toh kudin ma yana isan mutum ne. ga hidimar iyali da ta yan uwa marasa karfi, gaskiya Najeriya na cikin wani hali. Allah dai ya shige mana gaba.”

An hango tashin farashin kayayyaki

A wani labarin, mun ji cewa ana bayyana fargabar dorewar hauhawar farashin kayan abinci, kamar yadda aka dade ana fuskanta a tsawon lokaci a Najeriya.

Wannan na zuwa ne yayin da rahoto ya bayyana yiwuwar samun tsaiko ga ga kokarin nahiyar Afirka na cimma burin kawo karshen yunwa nan da shekarar 2030.

Asali: Legit.ng

Online view pixel