Gwamnan APC Ya Amince da Biyan N977m Kudin Jarabawar NECO Ga Dalibai 48,385 Na Jiharsa

Gwamnan APC Ya Amince da Biyan N977m Kudin Jarabawar NECO Ga Dalibai 48,385 Na Jiharsa

  • Gwamnan jihar Katsina Malam Umaru Dikko Radda ya waiwayi ɗaliban jihar da suka zana jarabawar NECO a shekarar 2023
  • Gwamnan ya fitar da kuɗaɗe har N977m domin biyan kuɗin jarabawar na ɗalibai 48,385 da suka zana jarabawar a faɗin jihar
  • Biyan kuɗaɗen jarabawar na NECO na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Katsina ta fitar a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya amince da fitar da Naira miliyan 977 (N977,023,000) don biyan kudin jarabawar NECO na shekarar 2023 ga ɗalibai 48,385 na jihar.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Katsina ta wallafa a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Ɗaya daga cikin ɗalibai mata na jami'ar tarayya da yan bindiga suka sace ta kuɓuta

Dikko Radda ya kudin jarabawar NECO a Katsina
Gwamna Dikko Radda ya amince da biyan N977m kudin jarabawar NECO Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Gwamna Radda ya biya kuɗin WAEC

Amincewa da fitar da kuɗin na zuwa ne wata guda bayan gwamnan ya amince da biyan N364.8m ga ɗaliban da suka zana jarabawar WAEC na jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya amince da biyan kuɗaɗen ne domin amfanar ɗalibai 20,000 ƴan asalin jihar da suka zauna jarabawar a shekarar 2023.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani ɗan jihar Katsina mai suna Alhassan Magaji wanda ya nuna jindaɗinsa kan wannan abin arziƙin da gwamnan ya yi.

"Wannan abun jindaɗi ne domin ya taimaki ƴaƴan talakawa waɗanda ba za su iya biyan kuɗaɗen ba saboda halin da ake ciki a yanzu." A cewarsa.

Ya bayyana cewa rashin biyan kuɗin da gwamnatin baya ta yi ya sanya yara da yawa sun dakata da cigaba da karatun su.

Ƴan majalisa sun yi watsi da ƙudurin hana biyan kuɗin NECO

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta amince da wani muhimmin nadin da Shugaba Tinubu ya yi

Majalisar wakilan tarayya ta yi watsi da wani kudiri da ya nemi a hakura da karbar kudin jarrabawar SSCE na shekarun 2023 da 2024.

Hon. Anamero Dekeri (APC Edo) ya kawo wannan kudiri a majalisar tarayya domin a saukakawa jama’a. Bayan muhawarar da aka tafka a zauren, ‘yan majalisar wakilai ba su yi na’am da hakan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng