Ikon Allah: Ɗaya Daga Cikin Ɗalibai Mata Na Jami'ar Tarayya da Yan Bindiga Suka Sace Ta kuɓuta

Ikon Allah: Ɗaya Daga Cikin Ɗalibai Mata Na Jami'ar Tarayya da Yan Bindiga Suka Sace Ta kuɓuta

  • Dakarun yan sanda sun samu nasarar ceto ɗaya daga cikin ɗalibai mata 5 da yan bindiga suka sace a jami'ar tarayya ta Dutsinma
  • Mai magana da yawun yan sandan Katsina, SP Abubakar Aliyu, ya ce a halin yanzun an kai ta asibiti domin duba lafiyarta
  • Ya ce hukumar yan sanda za ta yi amfani da duk kayan aikin da ake buƙata domin kuɓutar da ragowar ɗaliban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Ɗaya daga cikin ɗalibai mata na jami'ar tarayya ta Dutsinma a jihar Katsina da yan bindiga suka yi garkuwa da su ta shaƙi iskar 'yanci.

An ceto ɗaliba daya da yan bindiga suka sace a Dutsinma.
Daya Daga Cikin Daliban Jami'ar Tarayya Ta Kubuta daga hannun yan bindiga a Katsina Hoto: FUDMA
Asali: Twitter

Rundunar ƴan sandan jihar ce ta samu nasarar kubutar da ɗalibar a wani samame da ta kai ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnoni 3, Kotun daukaka kara ta tsaida ranar yanke hukunci kan zaben gwamnan APC

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina. SP Abubakar Aliyu, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ɗalibar, wacce aka ɓoye sunanta saboda dalilan tsaro, dakaru sun ceto ta ne a ƙauyen Bilbis da ke maƙwaftaka da jihar Zamfara.

Kakakin yan sanda ya jaddada kudirin rundunar na yin amfani da wadatattun kayan aiki don ganin an ceto sauran ɗalibai hudun da aka yi garkuwa da su.

SP Aliyu ya ce:

"A halin yanzu, ɗalibar da aka ceto tana samun kulawar likita, kuma hukumar ƴan sanda na miƙa godiya ga ɗalibar bisa kwarin guiwarta wajen taimakawa da bayanan sirri."

Yadda yan bundiga suka sace ɗaliban jami'ar

Idan baku manta ba, wasu ƴan ta'adda sun yi garkuwa da ɗalibai mata biyar na jami'ar tarayya da ke garin Dutsinma a ranar 4 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

Nasara: Dakarun sojoji sun buɗe wa tawagar 'yan bindiga wuta, sun kashe su da yawa a arewa

An ce an yi garkuwa da ɗaliban ne a gidansu da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri Memorial International daura da titin Tsaskiya.

Bayan faruwar lamarin, hukumar ƴan sanda ta fito ta bayyana cewa ta kama mutum ɗaya da zargin hannu a sace ɗaliban, rahoton Leadership.

Sojoji sun kashe yan bindiga a Kaduna

A wani rahoton na daban Sojojin rundunar OPSH sun halaka yan bindiga bakwai a ƙaramar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Oya James, ya ce sojojin sun kwato muggan makamai daga hannun yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel