Asiri Ya Tonu: Yadda Gwamnan APC Yake Bushasha da Biliyoyi Alhali Ana 'Babu Kudi'
- Gwamnatoci su na ta kukan babu kudi a kasar nan, amma da alama har yanzu ba su rage sharholiya ba
- Wasu kwangiloli da Babajide Sanwo Olu ya bada ya jawo an taso Gwamnatin jihar Legas a gaba da surutai
- Hukumar PPA ta bada aikin miliyoyi domin aikin ganye sannan an ware biliyoyi da sunan sayen fitulu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Lagos - Gwamnatin jihar Legas ta amince a kashe N44.8m domin aikin gyaran ganye a karkashin wani tsari da aka kawo a yankin Epe.
A makon nan Daily Trust ta bankado cewa wannan kwangila da aka ba kamfanin M/S Obak Nigeria Enterprises zai ci makudan miliyoyi.
Bayanan da aka samu daga hukumar PPA sun nuna tun a watan Mayu aka bada kwangilar lokacin da Babajide Sanwo Olu ya zarce.
Zargin facakar Gwamna Babajide Sanwo-Olu
A lokacin da gwamnati ta ke kukan babu kudi a kasa, Babajide Sanwo-Olu ya amince a kashe N7.5m wajen sayen turaren ruwa a ofishinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya yarda a kashe N3bn domin sayen fitilu aiki a ofishin mataimakinsa watau Obafemi Hamzat.
Sahara Reporters ta rahoto Obafemi Hamzat ya na cewa N3m kurum aka ware masa da nufin sayen wadannan fitilu, ba biliyoyin kudi be.
Sanwo-Olu zai kashewa hotunan Tinubu N70m
Mutane da-dama sun soki yadda ake facaka da kudi a daidai lokacin da talakawa yake kuka da tsadar rayuwa da hauhawan farashin kaya.
A kan hotunan Bola Tinubu da za a rika sagalawa a ofisoshi kuwa, jaridar ta gano cewa gwamnatin Sanwo-Olu ta amince a kashe N73.1m.
Kamfanin Flolizvi Connect aka ba aikin ta karkashin shugaban ma’aikatan fadar gwamna.
Gwamna zai saye motocin miliyoyi a Legas
Akwai N440.75m da aka amince domin sayen sababbin motocin Lexus LX 600 sannan an bada kwangilar kawo kaji 2000 a kan N18.5m.
400m aka ware domin catar jirgin sama sannan za a gyara wani cocin Angilikan da ke unguwar Oke-Popo, wannan aiki zai ci fiye da N580m.
Wasu sun kai Bola Tinubu kotu a Legas
Ana zargin cewa a cikin wadanda aka ba kujerar REC a INEC akwai cikakkun ‘yan jam’iyyar APC , labari ya zo cewa saboda haka aka je kotu.
Akwai wanda ake zargin ya goyi bayan Tinubu a zaben 2023, yanzu ya zama kwamishinan hukumar INEC, ana ganin hakan ya saba doka.
Asali: Legit.ng