Innalillahi: Tsohon Kwamishinan ’Yan Sanda a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Sifeta Ya Kadu
- Fatai Shittu, wanda ya yi kaurin suna lokacin da ya ke kwamishinan 'yan sanda a jihar Zamfara ya rasu a jiya Juma'a
- Babban Sifetan 'yan sanda, Kayide Egbetokun a madadin rundunar 'yan sandan ya tura sakon ta'aziyya ga iyalansa
- Marigayin kafin rasuwarshi ya yi aiki a jihohin Zamfara da Legas da Imo da Ebonyi da Ogun da Kebbi da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babban Sifetan 'yan sanda a Najeriya, Kayode Egbetokun ya nuna alhininsa bayan mutuwar Fatai Adio Shittu mai ritaya.
Egbetokun ya bayyana kaduwarsa ne a yau Asabar 18 ga watan Nuwamba na tsohon kwamishina 'yan sandan a Najeriya, Legit ta tattaro.
Yaushe Shittu ya rasu?
Rahotanni sun tattaro cewa Shittu ya rasu ne a jiya Juma'a 17 ga watan Nuwamba ya na da shekaru 73 a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce mutuwar Shittu wanda dan asalin jihar Kwara ne abin takaici ne.
Sanarwar ta ce:
"Kwamishina Shittu ya kasance mai kokari wurin gudanar da aikinsa inda ya ba da gudunmawa mai tarin yawa ga rundunar 'yan sanda.
"Kafin yin ritaya a watan Agustan shekarar 2011, marigayin ya rike mukamin kwamishinan 'yan sanda a Zamfara da kuma bangaren jin dadin al'umma.
Wasu jihohi Shittu ya yi aiki:
Sanarwar ta kara da cewa:
"Shittu ya shiga aikin dan sanda a shekarar 19 79 inda ya yi aiki a jihohin Zamfara da Kebbi da Ondo da Legas da Imo da Abuja da Edo da Delta da Ebonyi da sauransu."
An haifi Shittu a ranar 23 ga watan Agustan 1950 a Offa da ke jihar Kwara, marigayin ya karatun digiri a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zari'a inda ya karanta bangaren tarihi.
Tsohon gwamnan Ondo ya rasu
Kun ji cewa, tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Ondo, Manjo Janar Ekundayo Opaleye ya riga mu gidan gaskiya a Abeokuta.
Ekundayo ya mulki jihar Ondo da Ekiti a zamanin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida tsakanin shekarar 1986 zuwa 1987.
Asali: Legit.ng