Yan Sanda Sun Kama Barawon Shanu a Jigawa, Sun Gano Shanu a Gidansa

Yan Sanda Sun Kama Barawon Shanu a Jigawa, Sun Gano Shanu a Gidansa

  • Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar cafke wani barawon shanu tare da kwato shanu uku da aka sace a karamar hukumar Kiyawa, jihar Jigawa
  • Rundunar ta ce ta samu rahoton satar shanun ne a ranar 13 ga watan Nuwamba, inda jami'an rundunar suka bazama aiki, har suka gano inda barayin suke
  • Wanda rundunar tafke cafke, ya amsa laifin sa, yayin da rundunar ke ci gaba da bincike don kamo wadanda suka tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Jigawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ta ce jami’anta sun bi diddigi tare da gano wasu shanu guda uku da aka sace, a gidan Muktari Ibrahim da ke Sabuwar Unguwa, karamar hukumar Kiyawa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun daukaka kara ta tsayar da ranar Juma’a don yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano

DSP Lawan Shiisu Adam, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, ya shaida wa wakilinmu cewa, sun gano Ibrahim mai shekaru 23, biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu.

Rundunar 'yan sandan Najeriya
Rundunar ta tabbatar da kama mai laifin tare da wkato shanu uku da ya boye a gidansa Hoto: Nigerian Police
Asali: Twitter

Darajar shanu uku ta kai naira miliyan 1,150,000

Adam ya ce, a ranar 13 ga watan Nuwamba, da misalin karfe 8 na safe, wani Umar Musa da Idris Ismail daga kauyen Malamawa, karamar hukumar Kiyawa, suka kawo rahoton sace shanun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sa, mutanen sun bayyana wa hukumar cewa barayi da misalin karfe 3 na safe sun sace shanu uku a gidajensu wanda kudinsu ya kai naira miliyan 1,150,000, cewar rahoton Daily Trust.

An mayar da shanun ga masu su - Rundunar 'yan sanda

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin rundunar ya ce, Ibrahim ya bayyana masu cewa ya karbi shanun da aka sato daga hannun wani mutum mai suna Yusuf, tare da wasu mutane.

Kara karanta wannan

Yan bindigar da suka sace ma'aikacin CBN da wasu 2 suna neman N10m kudin fansa

Ya kara da cewa, rundunar ta kwato shanun tare da mayar da su ga mamallakan su, yana mai jaddada cewa hukumar ‘yan sanda na ci gaba da tsaurara bincike don cafke wadanda suka tsere daga cikin barayin shanun.

NSCDC ta cafke hatsabibin barawon shanu a Katsina

Ko a shekarar 2021, sai da hukumar tsaro ta NSCDC ta damke wani wanda ake zargin barawon shanu ne da wani mai safarar miyagun kwayoyi a jihar Katsina, rahoton Legit Hausa ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel