An Cafke Hatsabibin Ɓarawon Shanu Da Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi a Jihar Katsina

An Cafke Hatsabibin Ɓarawon Shanu Da Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi a Jihar Katsina

  • Hukumar NSCDC ta kama wani da ake zargin barawon shanu ne da kuma wani mai safarar miyagun kwayoyi a jihar
  • Jami’in hulda da jama’an hukumar na jihar, DSC Muhammad Tukur ya bayyana hakan a ranar Laraba
  • Rahotanni sun bayyana cewa barawon shanun mai shekaru 20 da haihuwa yana bai wa masu garkuwa da mutane bayanai

Jihar Katsina - Hukumar tsaro ta NSCDC ta ce ta damke wani wanda ake zargin barawon shanu ne da wani mai safarar miyagun kwayoyi a jihar Katsina, rahoton Daily Nigerian.

Jami’in hulda da jama’an hukumar na jihar, DSC Muhammed Tukur ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba a Katsina.

An Cafke Hatsabibin Ɓarawon Shanu da Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi a Jihar Katsina
Wanda ake zargi da safarar kwayoyi da satan shanu a Katsina. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Dagaci da mazauna kauye sun tsere bindi-zage bayan wani abin tsafi ya yi ajalin mutane 7 a Adamawa

A cewar sa, daya daga cikin su shekarun sa 20 kuma mazaunin kauyen Maikaho ne dake karkashin karamar hukumar Jibia, ana zargin sa da satar shanu da kuma bai wa ‘yan bindiga bayanai.

Wadanda ake zargin ‘yan wata kungiyar sa kai ne

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, Tukur ya ce:

“Wadanda ake zargin suna cikin wata kungiyar ‘yan sa kai dake kauyen Maikaho kuma ana zargin su da taimakon ‘yan bindiga, satar shanu da sauran miyagun laifuka.”

‘Yan sa kai da kansu suka mika shi ga hukumar NSCDC sannan yayin tambayar sa ya tabbatar da cewa tilasta shi barayin shanu su ka yi ya sato musu shanaye fiye da 10 da sauran dabbobi.

A cewar sa:

“Duk da dai ya musanta shiga harkar ta’addanci, ya tabbatar da cewa akwai wata kungiyar ‘yan bindiga da ta bukaci ya taya su ta’addanci amma ya ki amincewa.
“Ya bayyana mana cewa kungiyar ta yi garkuwa da mutane 3 a kauyen Falale inda suka nemi ya taya su aikin, daga baya su ka ba shi bindiga kirar AK-47 don ya ajiye musu."

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun koma dajin Kaduna – DSS ta ankarar da sauran hukumomi

Kakakin hukumar NSCDC ya ce har yanzu suna kara bincike akan lamarin kuma idan sun kammala za su tura su kotu don a yanke musu hukunci.

An kama dayan da wiwi da sauran kayan shaye-shaye

Dayan wanda aka kama yana da shekaru 29 da haihuwa kuma mazaunin Yangora ne dake karamar hukumar Bindawa ne. An kama shi da miyagun kwayoyi ciki har da wiwi da sauran su.

A cewar sa a baya yana sana’ar sayar da kayan sawa ne kuma yana komawa gida duk shekara don yin noma.

Hukumar NSCDC zata mika shi hannun hukumar NDLEA don su ci gaba da bincike akan sa kamar yadda Tukur ya bayyana.

Yayin da manema labarai su ke tambayar wadanda ake zargin, sun tabbatar da aikata laifukan da ake zargin su dasu, sai dai barawon shanun ya ce ba ya da hannu a garkuwa da mutane.

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna

A wani rahoton daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani hatsabibin dan damfara bisa zargin sa da amfani da sunan babban bankin Najeriya wurin yasar dukiyar mutane 64 ta hanyar amfani da takardun bogi, LIB ta ruwaito.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba, 8 ga watan Satumba inda yace an kama wanda ake zargin, Buhari Hassan a Yankaba Quarters ne da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel