Birnin-Gwari: Mutane da dama sun mutu a harin da yan ta'adda suka kai wajen biki

Birnin-Gwari: Mutane da dama sun mutu a harin da yan ta'adda suka kai wajen biki

- Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a kauyen Kakangi da ke Birnin Gwari a wani waje da ake gudanar da shagulgulan biki

- Yan bindigar sun fara bude wuta a wani ofishin 'yan sanda, kafin da ga bisani suka fara bi gida gida suna kashe mutanen da suka taras a ciki

- Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun mutu yayin da aka tabbatar da jikkatar mutane shida, cikinsu kuwa har da kananan yara

Rudani ya mamaye kauyen Kakangi da ke Kudu maso Yammacin karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, sakamakon wani hari da 'yan bindiga suka kai kauyen a ranar Asabar a wani waje da ake gudanar da shagulgulan biki.

Yan bindigar dai sun dira kauyen Kakangi da misalin karfe 5 na yamma a kan mashina, inda nan take suka bude wuta suna harbin kan mai uwa da wabi a wani ofishin 'yan sanda, kafin da ga bisani suka fara bi gida gida suna kashe mutanen da suka taras a ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun mutu yayin da aka tabbatar da jikkatar mutane shida, cikinsu kuwa har da kananan yara, wadanda aka garyzaya da su babban asibitin Birnin Gwari domin yi masu magani.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: A yau shugaba Buhari zai isa Dubai domin halartar muhimmin taro

Birnin-Gwari: Mutane da dama sun mutu a harin da 'yan ta'adda suka kai gidan biki

Birnin-Gwari: Mutane da dama sun mutu a harin da 'yan ta'adda suka kai gidan biki
Source: Facebook

Wani mazaunin garin da ya tsallake rijiya ta baya baya wanda kuma ya samu mafaka yanzu a kauyen Gagumi da ke kusankilomita 20 nesa da kauyensu na Kakangi ya bayyana yadda aka yi har ya kubuta.

"Muna zaune a kofar shiga ofishin 'yan sandan, sai kwatsam muka ga wasu 'yan ta'adda dauke da bindigogi, suna zuwa suka bude mana wuta. Na tsallake katanga na tsira da rayuwata. A yayin da nake tsaka da guduwa, na hango yadda hayaki ke tashi daga bangarori da dama na garin," a cewarsa.

Wani mazaunin garin Birnin Gwari da ya bukaci a sakaya sunanshi, ya ce, "Muna bukatar taimako a Birnin Gwari saboda ana kashe 'yan uwanmu ba dare ba rana. Ku kalli kisan gillar da aka yiwa jama'a a kauyen Kakangi a ranar Asabar," a cewarsa.

Da ya ke tabbatar da faruwar kai harin, Ibrahim Abubakar Nagwari, shugaban kungiyar sa kai kan zaman lafiya da shugabanci na gari na karamar hukumar Birnin Gwari a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ya ce 'yan ta'addan sun cinnawa gidaje da dama wuta a kauyen.

Duk wani yunkuri na tuntubar mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar DSP Yakubu Sabo ya ci tura.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel