Wasu Sun Sace Wayar Tsohon Minista a Kotu Wajen Sauraron Shari’ar Zaben 2023

Wasu Sun Sace Wayar Tsohon Minista a Kotu Wajen Sauraron Shari’ar Zaben 2023

  • Kotun daukaka kara ta zauna domin sauraron shari’ar zaben Gwamna Abdullahi Sule da David Ombugadu a birnin tarayya Abuja
  • Bayan mai shari’a U. Onyemenam ya gama jagorantar zaman, sai aka lura an dauke wayar salular Labaran Maku a babban kotun
  • An yi ta lalube, amma haka aka bar kotu ba tare da an yi iya gane inda wayar tsohon Ministan na Goodluck Jonathan ta shiga ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ana zargin wayar salular Labaru Maku ta bace yayin da ya shiga kotun daukaka kara da ke zama a garin Abuja.

Lamarin kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto a yammacin Laraba, ya faru yau dinnan ne, 15 ga watan Nuwamba 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Kaduna za ta birne gawarwakin mutane 60

Shari'ar zaben Gwamna a Nasarawa a kotu

Maku ya nemi takarar gwamnan jihar Nasarawa, amma daga baya ya janye kuma ya goyi bayan David Emmanuel Ombugadu.

Labaran Maku
An sace wayar Labaran Maku a kotu Hoto: @RealLabaranMaku
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanzu haka ana shari’a ne tsakanin David Ombugadu da Mai girma Abdullahi Sule wanda kotun korafin zabe ta tsige daga kan mulki.

Wanenen Labaran Maku?

A 2015 da 2019, tsohon Ministan yada labaran ya yi harin kujerar gwamna har ya yi takara a jam’iyyar APGA, sai dai bai yi nasara ba.

Mista Maku sanannen ‘dan siyasa ne domin ya rike tun daga Kwamishina har zuwa mataimakin gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007.

Wayar Maku ta yi kafa a kotu

Magoya baya da mukarraban Maku sun yi ta lalubawa ko za a gano wayar, amma haka aka bar harabar kotun ba tare da an dace ba.

Rahoton ya ce an yi ta kokarin kiran lambar ‘dan siyasar domin gano inda salular ta shiga, har aka bar babban kotun ba a ji karar ta.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi barna a Kaduna, sun sungume Hakimi a sababbin hare-hare

Satar wayar manya a kotu

A lokacin da ake shari’ar zaben shugaban kasa, mutane sun yi ta yada jita-jita cewa wasu sun yi gaba da wayar Peter Obi a cikin kotu.

Sai dai da alama babu kanshin gaskiya a rade-radin, ‘dan takaran na LP bai taba fito ya na cigiyar wayarsa da ake shari’ar zaben ba.

Wanene ya lashe zaben Gwamna a Nasarawa?

Kotun daukaka kara ta gama sauraron karar zaben Nasarawa, ana a labari cewa hukunci ya rage a zartar tsakanin PDP da APC mai-ci.

Kotun da ke sauraron kararrakin zaben gwamnoni ta na nan a yankin Three Arms Zone, a hanyar Shehu Shagari a babban birnin na Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel