Tarihin Muhammad Indimi

Tarihin Muhammad Indimi

Shi dai Muhammadu Indimi wanda ya kasance suruki ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, sanadiyar aure dake tsakanin 'ya'yan su, Zahra Buhari da Ahmed Indimi da aka gudanar a watannin da suka gabata.

An haifi Dr Muhammadu Indimi a watan Agustan shekarar 1947 a jihar Borno dake Najeriya, kuma shi dan kasuwa ne wanda ya kafa kuma ya samar da kamfanin man fetur da ma'adanansa na Oriental Energy Resources a shekarar 1990, wanda har ila yau shi yake shugabancin kamfanin.

A shekara ta 2014, mujallar Forbes ta jero sunan Muhammad Indimi a matsayin mutum na 37 da yafi kowa arziki a nahiyar Afirka.

Alhaji Indimi mutu ne shiru-shiru wanda bai fiye magana ko hayaniya ba, amma ya kware a yarukan Kanuri, Turanci da kuma Hausa.

Tarihin Muhammad Indimi
Tarihin Muhammad Indimi

Ya fito ne daga gundumar Fezzan ta garin Maiduguri a jihar Borno kuma yana da dangantaka ta 'yan uwa a jihar Kano. Ya tashi daga gundumar Fezzan zuwa wata unguwa da ake kira Millionaires quaters a birnin Maiduguri, a tsakiyar shekarar 1980, kuma daga bisani ya koma wata unguwa a hanyar Damboa a shekarar 1990, inda ya gina katafaren gida tare da tafkeken masallaci (Masallacin Indimi).

KU KARANTA: Makiyaya na Fulani sun fyade wata tsohuwa mai shekaru 72 har ta fita hayyacinta

Ya taba yin aiki a karkashin hamshakin mai kudin nan na Maiduguri, marigayi Alhaji Mai Deribe a cikin shekarun 1970 har zuwa farkon 1980. Yana kuma da dansa da aka sanya masa sunan bayan Alhaji Mai Ahmad Deribe ya shude.

Tare da shi da tsohon shugaban kasar Amurka, Mr. W. Bush, sun kafa kamfanin man fetur na M & W Pump tare da gina ofisoshi a garuruwan Maiduguri da Enugu a nan Najeriya.

Alhaji Muhammad Indimi ya samu wanzuwa inda aka ba shi kwali na digiri da kuma diplomasiyya daga jami'o'in kasar nan da kuma na ketare.

Abin dogaro na sana'ar shi a yanzu: Shugaban kamfanin man fetur na Oriental Energy Resources

Ya dukufa wajen kyautatawa al'umma da bayar da sadaka ga mabukata, don ko yanzu yana gina gidaje guda 100 karkashin gidauniyar sa ta tallafi domin tallafawa wadanda rikicin Boko haram ya salwantar da muhallansu.

KU KARANTA: Boko Haram sun kaiwa ayarin Sojin kasa wani hari na bazata a jihar Borno

Akwai wasu gidaje 100 da a yanzu haka ake ginawa a jihar Akwa Ibom domin rabewa ma'aikatan kamfanin sa.

A baya ya bayar da taimakon injinan samar da wutar lantarki ga asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri a tsakiyar shekarar 1990 lokacin da samar da wutar lantarki ya zama matsala mai tsanani sannan kuma ya bayar da gudunmawa ga yawancin al'ummomi a Borno da wajen Borno ciki har da bayar da taimako na kudi ga jami'ar kimiyya da fasaha ta birnin Minna dake jihar Neja da kuma jami'ar Tafawa Balewa ta jihar Bauchi da ire-iren su.

Iyalan sa:

Matan sa: Akwai Fatima Indimi wadda ya aura tun a shekarar 1975 kuma suna nan tare da kuma matar sa ta biyu, Do'aa Indimi, ita kuma ya aure ta ne a shekarar 1993, kuma sunan itama mutu ka raba takalmin kaza.

Yana da 'ya'ya guda ashirin da ya same su ta hanyar wannan matan nasa guda biyu kuma yana da jikoki wanda adadin su ya kai 16.

KU KARANTA: Labarai cikin Hotuna: Shugabannin jam'iyyun APC da PDP sun kaiwa Shugaba Buhari ziyarar ban gajiya

Indimi mutum ne mai kirki kuma mai son iyalansa, domin ba shi da wani buri a rayuwa face ya bayar da lokacin sa ga iyalansa, 'ya'yansa da kuma jikoki.

Muhammad Indimi a karan kansa, suruki ne ga marigayi Alhaji Mustafa Haruna na gundumar Hausari dake garin Maiduguri. Da yawa daga cikin 'ya'yansa kuma surukai ne ga manya a kasar nan domin kuwa sun hada dangantaka da ministoci, shugabannin kasa, gwamnoni da kuma 'yan kasuwa.

Abin soyuwa da kuma debe kewa a gare shi:

Indimi ya kasance mutum ne mai son sukuwa akan doki, domin kuwa a tsakanin shekarun 1980 zuwa 1990 ya dauki nauyin hada gasar sukuwa akan dawakai a birnin Maiduguri kuma shi kan shi yana da tarin dawakai masu dinbin yawa.

Sanadiyar son sukuwa akan doki ne ya sanya shi ya zagaye filin Ramat da gini na bulo wanda ake kira da filin sukuwa a yanzu a birnin na Maiduguri.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng