Dangote Ya Samu Matsala Yayin da Ya Rasa $69m a Rana, Attajirin Habasha Ya Yi Sama da $8.5b
- Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya samu matsala bayan tafka mummunan asara har dala miliyan 69 a kwana daya kacal
- Har ila yau, attajirin kasar Habasha Mohammed Al Moudi ya samu kazamar ribar fiye da dala biliyan 3 da doriya
- Hakan ya bai wa Al Moudi damar haye wa kan Rupert Johann na kasar Afirka ta Kudu wanda a baya ya ke sama da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Dan kasar Habasha, Mohammed Al Moudi ya samu kazamar ribar biliyoyin daloli inda ya samu dala biliyan uku.
Attajirin ya samu karin kaso 61 cikin dari cikin kasa da kwanaki talatin kacal yayin da Aliko Dangote ya tafka babbar asara, Legit ta tattaro.
Mene Bloomberg ke cewa kan masu arzikin?
Bloomberg ta ruwaito cewa Al Moudi na da yawan arziki dala biliyan 5.24 a farkon makwanni biyu na watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma zuwa wannan wata da mu ke ciki na Nuwamba ya samu karin dala biliyan 3.25 a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba.
Attajirin mai shekaru 77 ya na da kadarori da yawa a kasashen Sweden da Saudiyya da kuma Habasha.
Mene makomar Aliko Dangote a jerin masu kudin?
Al Moudi yanzu ya zarta dan kasar Afrika ta Kudu Johann Rupert da yawan arziki har dala biliyan 8.3.
Har ila yau, mafi yawan arziki a Nahiyar Afirka, Aliko Dangote ya samu tasgaro a arziki inda ya sauko har mataki na 115 a jerin masu kudin duniya.
Dangote ya samu matsaloli tun a watan Yuni bayan Shugaba Tinubu da bankin CBN sun kawo sabbin tsare-tsare kan naira.
Attajirin ya yi asarar dala miliyan 69 a ranar Talata 14 ga watan Nuwamba na wannan shekara inda masana ke cewa hakan na da nasaba da matsalolin naira.
Rabiu ya ci ribar N1.5b a awanni 24
A wani labarin, attajiri, Abdussamad Rabiu ya samu ribar fiye da naira biliyan daya a cikin awanni 24 kacal.
Bloomberg ya ruwaito cewa attajirin ya samu ribar wanda a yanzu ya kasance ya na da kudi har dala biliyan 5.98.
Asali: Legit.ng