Watanni da Kaddamarwa, Rashin Mai Ya Jawo Dangote Bai Iya Fara Fitar da Fetur ba

Watanni da Kaddamarwa, Rashin Mai Ya Jawo Dangote Bai Iya Fara Fitar da Fetur ba

  • An gama gina wasu kananan matatu domin tace danyen mai a Najeriya, sai dai abin ba kamar yadda ake tunani ba ne
  • Sakacin gwamnati ya yi sanadiyyar da matatun ba su samun kayan da za su yi aiki, sai dai a nemo mai a kasashen waje
  • Duk da Najeriya ta na da albarkatun mai a Neja-Delta, NNPC ya shiga yarjejeniya da wasu kamfanonin dabam a Duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Rashin samar da danyen mai ga kanana da manyan matatun Najeriya ya kawo matsala wajen tace mai, a daina dogara da kasashen waje.

Punch ta ce har yanzu Najeriya ta na shigo da mai ne daga kasashen waje bayan an fita da danyen man, wanda hakan abin kunya ne ga kasar Afrikar.

Kara karanta wannan

"Ya ban ga kowa ba a 2go?" Dan Najeriya da ya shafe shekaru 15 a yari ya yi tambaya mai ban dariya

Tun tuni aka kaddamar da matatar Dangote kuma ake sa ran za ta fara aiki, a karshe har sabon lokacin da aka tsaida watau Oktoba ya wuce a haka.

Dangote
Ba a samun fetur a matatar Dangote Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu danyen man da Dangote za su tace

Kusan matatu biyar aka gama ginawa, abin da kawai ake jira shi ne su fara aiki, abin da ya hana su fara tace mai a Najeriya shi ne rashin danyen mai.

Duk da Najeriya ta na da arzikin mai, danyen man da kamfanin NNPC ya ke hakowa ya na tafiya ne wasu kasashe, dole Dangote ya nemo na shi dabam.

...sai dai Dangote ya fara da ganga 370, 000

Wani babban ma’aikacin Dangote, Devakumar Edwin ya shaida cewa za su fara da tace ganguna 370, 000, matatarsu za ta iya daukar 650, 000 a rana.

Kara karanta wannan

An yi ruwan daloli, bidiyo ya nuna yadda attajiri ya hau jirgi ya sako kudi, an yi warwaso

Idan an tace gangunan man, za a samu fetur, dizil, man jirgin sama da sauransu a gida.

Shugaban kamfanin na Dangote ya ce a karshen Nuwamban 2023, za su fitar da kayan farko da aka tace, abin da ake jira kurum shi ne danyen man.

Za a fita neman danyen mai a kasar waje?

Rahoton ya ce wasu ma’aikatan matatar Dangote sun ziyarci hukumar NUPRC, su ka koka da cewa ba su samun mai kuma bai dace su je nema a ketare ba.

Shugaban CORAN, Olusegun Ilori ya ce akwai kananan matatu akalla biyar da a shirye su ke da su fara aiki, amma ana ta samun cikas har zuwa yau.

Gwamnatin tarayya ta ce abin da ya jawo wannan shi ne rashin hako mai sosai a halin yanzu.

Wani da ya ke da karamin matata ya ce manyan kamfanoni sun fi sha’awar su fita da danyen mai waje, su samu dalolinsu a maimakon kasar nan ta cigaba.

Kara karanta wannan

Ya kamata CBN ta sa a daina amfani sabbin takardun Naira da Buhari ya kawo, malami ya fadi dalilai

Facaka bayan an cire tallafin fetur

Watanni 5 da hawa mulki, sai ga labari cewa Shugaban Najeriya zai batar da kusan N10bn a kan gyaran gidajen fadar shugaban kasa da na EFCC.

Za a gyara gidan shugaban kasa da ke Legas duk da fadar shugaban kasa ta koma Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng