Ba Haka Muka Yi Namu Ba, Oshiomole Ya Yi Martani Kan Tsarin NLC, Ya Ba Ta Shawara

Ba Haka Muka Yi Namu Ba, Oshiomole Ya Yi Martani Kan Tsarin NLC, Ya Ba Ta Shawara

  • Sanata Adams Oshiomole ya caccaki tsarin yadda kungiyar NLC ta dawo ta siyasa yayin gudanar da yajin aikinta
  • Oshiomole wanda tsohon shugaban kungiyar ce ya ce bai kamata kungiyar ta saka siyasa a gwagwarmayar ta ba
  • Ya ce kamata ya yi su fahimci cewa yanwar da ke damun ma'aikatan Tarayya bai fi na jihohi da kanannan hukumomi ba

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kungiyar NLC, Adams Oshiomole ya soki tsarin yadda kingiyar ke gudanar da harkokinta a yanzu.

Adams ya ce kwata-kwata kungiyar ba ta na yi don moriyar 'yan Najeriya da ma'aikatanta ba ne, cewar Punch.

Oshiomole ya soki NLC kan mayar da gwagwarmayarta ta siyasa
Oshiomole ya yi martani kan tsarin NLC a yanzu. Hoto: Adams, O/ Joe Ajaero.
Asali: Facebook

Mene Oshiomole ke cewa kan NLC?

Kara karanta wannan

Ruguntsumi yayin da NLC ta garkame mambobin Majalisar Tarayya a Abuja, ta yi abu daya

Oshiomole wanda a yanzu Sanata ne da ke wakiltar Edo ta Arewa ya rike shugaban NLC daga 1999 zuwa 2007, Newsnow ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya bayyana haka ne a yau Talata 14 ga watan Nuwamba a Abuja inda ya ce NLC ta kauce wa abin da ya kamata ta na yi.

Ya ce a kamata su matsa wa gwamnatocin jihohi su tabbatar da mafi karancin albashi da kuma walwalar ma'aikata a kasar, cewar Newstral.

Wane shawara Oshiomole ya bai wa NLC?

Ya ce:

"Zan goyi bayan duk wani mataki da zai inganta walwalar al'umma da kuma rage yunwa amma matsalar wannan yajin aiki ba don haka ba ne.
"Ya kamata mu yi hankali kada mu hada siyasa da wannan gwagwarmaya saboda matsalolin da ma'aikata ke fuskanta da yawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bada mamaki, ya kai ziyarar bazata Asibitin da aka kwantar da babban jigo

"Gwamnatin Tarayya ta ba da kyautar kudi naira dubu 35 amma bai kamata ace iya ma'aikatan Gwamnatin Tarayya ba ne kadai."

Oshiomole ya ce akwai ma'aikata a gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi wanda su ma su na fama da yunwar da na Tarayya suke da ita.

Kungiyar NLC ta rufe Majalisar Tarayya a Abuja

A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta NLC, ta rufe mashigar Majalisar Tarayya a Abuja a yau Talata 14 ga watan Nuwamba.

Kungiyar ta dauki matakin ne yayin da ta umarci tsunduma yajin aiki a kasar inda ta rufe mambobin Majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel