Hatsabiban Yan Bindiga Sun Gamu da Ajalinsu Yayin da Suka Kai Hari a Jihar Arewa

Hatsabiban Yan Bindiga Sun Gamu da Ajalinsu Yayin da Suka Kai Hari a Jihar Arewa

  • Yan bindiga huɗu sun bakunci lahira yayin da suka kai farmaki kauyen Ɗan Umaru a jihar Kebbi ranar Litini
  • Jami'an rundunar ƴan banga ne suka yi nasarar halaka ƴan bindiga bayan sun musu kwantan ɓauna
  • Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Jami'an tsaro ƴan sa'kai waɗanda aka fu sani da 'yan banga ko 'yan bijilanti sun samu nasarar halaka yan bindiga huɗu a jihar Kebbi, Arewa maso Yamma.

Yan banda sun halaka yan bindiga a Kebbi.
Nasara daga Allah: Yan Banga Sun Halaka Yan Bindiga Huɗu a Jihar Kebbi Hoto: Punchng
Asali: UGC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ƴan bangan sun murƙushe yan bindigan ne yayin da suka farmaki wani mutumi a ƙauyen Ɗan-Umaru, yankin Bena a jihar Kebbi ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar Gwamnatin jihar arewa, sun tafka mummunar ɓarna tare da sace mutane

Sakataren watsa labaran gwamnan jihar, Ahmed Idris ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Litinin a Birnin Kebbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris ya ce wannan nasara da aka samu ta fito ne daga bakin babban daraktan tsaro na majalisar zartarwa ta jihar Kebbi, AbdulRahman Usman.

Yadda aka kashe maharan gaba ɗayansu

Ya ce ‘yan banga sun dauki matsayi tare da kashe ‘yan bindigar a lokacin da suka kai farmaki wani kauye da ke kusa da Dan-Umaru mai iyaka da ƙauyen Dadin Duniya a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Ya kara da bayanin cewa a halin yanzu mutumin da harin ya shafa na kwance ana duba lafiyarsa a wani asibiti da ba a bayyana ba.

A kalamansa ya ce:

"Lokacin da 'yan bindigan suka kaddamar da hari a ƙauyen, cikin hanzari 'yan bangan suka ɗauki matsaya, kana suka ɗana wa maharan tarko suka sheƙe su dukka huɗun."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi garkuwa da shugabar ƙaramar hukuma a jihar Arewa

"Gawarwakin yan bindigan na can a ƙauyen Ɗan Umaru amma lamarin ya faru ne a kusa da ƙauyen wanda ke iyaka da ƙauyen Dadin Duniya na ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara."

An sace fasinjojin motar Gwamnatin Benue

A wani rahoton na daban kuma Miyagun ƴan bindiga sun sace mutane 13 daga motar kamfanin sufuri ta Gwamnatin jihar Benuwai.

Shaidu sun bayyana cewa maharan sun tare motar Bas ɗin a titin Naka zuwa Makurdi ɗauke da fasinjoji 16, uku suka tsira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel