NLC: Yayin da Ake Ci Gaba da Yajin Aiki, an Bayyana Yawan Ma'aikatun Da Ke Ciki Tsundum

NLC: Yayin da Ake Ci Gaba da Yajin Aiki, an Bayyana Yawan Ma'aikatun Da Ke Ciki Tsundum

  • Kungiyoyi da dama sun ba da hadin kai yayin da ake ci gaba da yajin aiki a Najeriya bayan cin zarafin Ajaero
  • Kungiyar NLC ta umarci shiga yajin aikin ne bayan cin zarafin shugaban kungiyar, Joe Ajaero a birnin Owerri na jihar Imo
  • Kungiyoyin da suka ba da hadin kai akwai na lafiya da ma'aikatan banki da wutar lantarki da makarantu da sauran manyan kungiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake ci gaba da bin umarnin kungiyar NLC, kungiyoyi da dama sun fada yajin aikin a yau Talata.

A yau Talata 14 ga watan Nuwamba NLC ta umarci dukkan ma'aikata su fantsama yajin aiki kan cin zarafin shugabanta, Joe Ajaero a Owerri.

Kara karanta wannan

Ruguntsumi yayin da NLC ta garkame mambobin Majalisar Tarayya a Abuja, ta yi abu daya

Kungiyoyin da suka bi umarnin kungiyar NLC wurin shiga yajin aiki
Kungiyoyi da dama sun tsunduma yajin aiki a Najeriya. Hoto: NLC.
Asali: Twitter

Wasu kungiyoyi ne suka shiga yajin aikin a Najeriya?

Daga cikin kungiyoyin da suka bi umarnin akwai Kungiyar masu siyar da abinci da kungiyar ma'aikatan ruwa (MWUN) da kuma ma'aikatan wutar lantarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da kungiyar malaman Kwalejin Fasaha (ASUP) da kuma manyan ma'aikatanta na SSANIP, Vanguard ta tattaro.

Har ila yau, akwai kungiyar ma'aikatan lafiya da kuma ma'aikatan bankuna da sauran hukumomin kudade a kasar.

Mene dalilin yajin aikin a Najeriya?

Wannan na zuwa bayan cin zarafin shugaban NLC, Joe Ajaero a Owerri babban birnin jihar Imo a makon da ya gabata, cewar gidan talabijin na Channels TV.

An ci zarafin Ajaero ne yayin da suke zanga-zanga a sakatariyar kungiyar da ke Owerri inda jami'an 'yan sanda suka kwamushe shi.

Wasu na ganin an kirkiri zanga-zangar ce ta Owerri don hana Gwamna Hope Uzodinma zarcewa a kan kujerarshi ta gwamna.

Kara karanta wannan

Yajin aikin gama gari: Ma’aikatan Taraba sun bijire wa umurnin NLC, kowa ya tafi wajen aiki

NLC ta rufe Majalisar Tarayya

A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta rufe mashigar Majalisar Tarayya a Abuja a yau Talata 14 ga watan Nuwamba.

Kungiyar ta kulle Majalisar ce tare da hana dukkan ma'aikata da sauran baki a harabar Majalisar fita daga wannan wuri

Wannan na zuwa ne yayin da NLC ta umarci tsunduma yajin aiki na gama-gari kan cin zarafin shugabanta, Joe Ajaero.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.