Amarya Ta Hade Fuska Yayin da Ta Ki Taka Rawa da Angonta a Wajen Bikinsu, Bidiyon Ya Girgiza Intanet
- Wata amarya ta bayyana a wajen bikinta cikin bacin rai ta yadda har ta ki yarda ta taka rawa a yayin shagalin bikin
- Da aka bukaci ta taka rawa, amaryar ta tsaya kikam sannan ta ki motsawa duk da kulawar da mijin ya nuna a filin rawan
- Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun tambaya ko dole aka yi wa matar don ta auri mutumin wanda shima alamu sun nuna baya farin ciki
Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wata amarya da ta ki taka rawa da mijinta a yayin shagalin bikinsu.
Saboda halin da amaryar ta nuna, mutane da dama da suka ga bidiyon suna ta tambayar ko dole aka yi mata don ta auri mutumin.
A wani dan gajeren bidiyo, wanda @ruzizilaplume ya wallafa, amaryar ta tsaya kikam ko motsawa bata yi lokacin da ya kamata ita da angon su taka rawa da murna a filin biki.
Ta tsaya a gefen mutumin sannan ta yi kicin-kicin da fuska kamar dai wani ya fusata ta a wajen bikin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hatta ga mijinta ya lura da halin da take nunawa sannan ya yi kokarin rike hannayenta, amma hakan bai yi tasiri ba. Shima, sai ya hade fuska kamar dai yana fushi da kasancewarsa a wajen bikinsa.
Mutumin shima, ya ki taka rawa sosai kuma wannan halaye nasu ya bai kowa mamaki a soshiyal midiya wadanda suka ce sun shiga rudani kan dalilin da yasa basu nuna jin dadinsu ba.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani ga amaryar da ta ki rawa da mijinta
@Goodjob ya ce:
"Ku fahimtar da ni abun da ke faruwa a nan."
@okebest musical ya tambaya:
"Shin dole ne sai an yi auren?"
@MKD ya ce:
"Dole aka yi maku a auren idan ba haka ba."
@Mbambu Constance:
"Hajiya, ki yi farin ciki ranarki ce, kuma sau daya take zuwa."
@marianie mereus:
"Matar na tunanin tsohon saurayinta."
Gobara ta halaka mutane ana cikin biki
A wani labarin kuma, mun ji cewa sama da mutum 100 ne suka kwanta dama yayin da wasu 150 suka jikkata sakamakon tashin gobara a wani bikin aure a gundumar Hamdaniya da ke lardin Nineveh na kasar Iraki.
BBC Pidgin ta ruwaito cewa daruruwan mutane ne ke hallara a wurin daurin auren a Qaraqosh da ke Arewacin lardin Nineveh na kasar Iraki lokacin da wata gobara ta kama wurin da yammacin ranar Talata 26 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng