Jerin manyan Jami’o’in da ake ji da su a Duniya a 2018
- An fitar da Makarantun da su ka fi kyau a Duniya
- A yanzu haka babu kamar Jami’ar Oxford ta Ingila
- Makarantun yawanci su na Amurka ne da Birtaniya
Mun kawo maku Jerin manyan Jami’o’in da ake ji da su a Duniya a wannan shekarar da aka shiga ta 2018. Mafi yawan Jami’o’in da su kayi zarra su na Kasar Amurka ne da kuma Kasar Ingila.
Jami’ar Oxford da ke Kudu maso gabashin Kasar Ingila ce a gaba sannan kuma Jami’ar Cambridge ta kasar. Bayan nan kuma sai irin su Jami’ar Stanford, MIT, Harvard da ke Kasar Amurka kamar yadda Times Higher Education ta bayyana.
KU KARANTA: Gwamnan Sokoto zai horar da Malaman Makaranta
Fitacciyar Makarantar nan ta fasaha da ke Kasar Switzerland watau Swiss Federal Institute of Technology ce ta zo ta 10 a jerin.
1. Oxford
2. Cambridge
3. CIT
4. Stanford
5. MIT
6. Harvard
7. Princeton
8. Imperial College
9. University of Chicago
10. Swiss Federal Institute of Technology
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng