Babu Ruwana, Ban Ce Za Mu Binciki Tinubu Kan Kudin Tallafin Fetur ba – ‘Dan Majalisar APC

Babu Ruwana, Ban Ce Za Mu Binciki Tinubu Kan Kudin Tallafin Fetur ba – ‘Dan Majalisar APC

  • Yusuf Adamu Gagdi ya nesanta kan shi daga zargin da ake yi masa na bada shawarar a binciki Bola Ahmed Tinubu
  • Gwamnatin tarayya ta janye tsarin tallafin man fetur, hakan ya ba Tinubu samun karin biliyoyin kudi a cikin baitul mali
  • ‘Dan majalisar ya yi karin haske kan rahotannin da ake yadawa, yake cewa shawara ya bada a rika taka-tsan-tsan

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaban kwamitin sojojin ruwa a majalisar taraya, Yusuf Adamu Gagdi ya musanya batun bincike a kan Bola Ahmed Tinubu.

The Guardian ta rahoto Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya na cewa babu inda ya fito ya ce za a binciki shugaban kasa game da kudin tallafin fetur.

Kara karanta wannan

Farfesa Yakubu Yana Fuskantar Barazanar Zuwa Gidan Yari a Kujerar Shugaban INEC

Wani jawabi da ‘dan majalisar na Filato ya fitar ya karyata rahoton da yake jaridu.

TINUBU
Bola Tinubu da shugaban majalisa Hoto: @NTANewsNow
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Ahmed Tinubu ya janye tsarin biyan tallafin man fetur, a baya an rahoto Hon. Gagdi ya na cewa za a duba inda kudin nan su ka shiga.

'Dan majalisa ya bukaci binciken Tinubu?

Kwatsam sai aka ji ‘dan majalisar Filaton ya musanya labarin, ya na mai kira ga gidajen jaridu su zama masu gaskiya idan an yi hira da su.

"Martabar ‘yan jarida na da muhimmanci, saboda ka da mu cefanar da ita da komai.
Wannan ya fito karara a labarin da ke yawo a bangaren jaridu ana zargin cewa na ce za a binciki shugaban kasarmu kan tallafin man fetur.
Babu abin da yake nesa da gaskiya kamar wannan rahoton."

- Hon. Yusuf Adamu Gagdi

Kara karanta wannan

Wayyo Gida Na: Jigon PDP Ya Kai Kuka, Gwamnatin APC Za Ta Rusa Masa Muhalli

Gagdi ya ce shi yabi Tinubu ne

Punch ta rahoto Gagdi ya ce ya yi hira ne da BBC Hausa, a nan ya nuna akwai bukatar cire tallafin fetur saboda wasu tsiraru kadai ake azurtawa.

‘Dan siyasar ya nuna a hirar da aka yi da shi, ya jinjinawa Bola Tinubu a kan namijin kokarin da ya yi wajen yin fatali da tsarin tallafin na mai.

A cewar Gagdi, ya bukaci a kara tsantseni wajen kashe dukiyar al’umma da ta taru a sakamakon daina biyan tallafin, ba wai a shirya bincike ba.

Dauda v Matawalle sun fallasa juna

Tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya zargi Dauda Lawal Dare da karya da yaudara kafin mulki ya shihgo hannunsa a bana.

Ministan tsaron ya ce Gwamnan ya taba yaudarar da shi, ya ba shi kwangilar taki, amma ya saba alkawari baya ga neman lakume wasu N300m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng