Ana ta Surutu Yayin da Tinubu Ya Yi Nade Naden Mukamai 5 a Kwana 1 Yana Saudi

Ana ta Surutu Yayin da Tinubu Ya Yi Nade Naden Mukamai 5 a Kwana 1 Yana Saudi

  • Bola Ahmed Tinubu ya cigaba da nade-naden mukamai a gwamnatinsa ko da ya yi tafiya zuwa kasar Saudi Arabiya
  • Yayin da shugaban Najeriyan ya ke halartar taron hadin-kan Saudi da Afrika, an fitar da sanarwar nadin mukamai
  • Akwai mutane biyar da su ka zama Hadiman shugaban kasa bayan shugabannin hukumar NPC 20 da aka nada

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Legit da ta bi mukaman da aka bada, ta lura mutane da-dama sun koka game da adadin wadanda su ke aiki da sabuwar gwamnati.

A lokacin da ake tunani za a tsuke bakin aljihu saboda kukan rashin kudi, sai aka ga shugaban kasa ya na ta faman nada mukamai iri-iri.

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya a kasar Saudi Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

Su wanene Bola Tinubu ya ba mukami?

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya tuno MKO Abiola, ya ba ‘diyarsa mukami a Fadar Shugaban Kasa

1. Ayomide Adeagbo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwa ta zo cewa Ayomide Adeagbo ya zama mai bada shawara na musamman a kan fasaha, al’adu da tattalin arzikin kirkire-kirkire.

2. Titilope Gbadamosi

Ita Titilope Gbadamosi ta zama mai taimakawa ta musamman wajen duba da sa ido a kan manufofin matasa da gwamnati ta fito da su.

3. Asefon Sunday Adedayo

Kwamred Asefon Sunday Adedayo ya zama sabon babban mai taimakawa shugaban Najeriya a kan harkar tattaunawa da dalibai.

4. Ms. Rinsola Abiola

Ita kuwa Rinsola Abiola ta samu aikin babban mai bada shawara a kan harkokin shugabanci da ‘yan kasa a gwamnatin Bola Tinubu.

5. Mohammed Isa

Ajuri Ngelale ya sanar da cewa shi kuwa Mohammed Isa ya zama babban mai taimakawa Mai girma shugaban kasa kan harkokin masu nakasa.

Abin da mutane ke fada a kan Tinubu

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Tinubu ya amince da sabbin nade-nade 20, jerin sunaye

Irinsu @kuwait_magix sun soki nade-naden musamman na Asefon S. Adedayo, su ka ce wadanda aka ba mukamai sun fi ‘yan kasar yawa.

Rinu Oduala ta ce Kwamred Asefon Sunday Adedayo da aka nada ya kai kusan shekaru 50, ta na ganin bai dace da harkar zama da dalibai ba.

Shi kuwa wani yake cewa a yadda ake tafiya, adadin wadanda Tinubu ya ba mukamai sun isa su aukawa wata karamar kasar Afrika da yaki.

Tinubu ya ba Hannatu Musawa mukami

Ayomide Adeagbo ya canji Hannatu Bala Musawa wanda ta zama Minista a bangaren.

A lokacin da ake tantance ta amajalisa, an ji labari Hannatu Bala Musawa ta sharba kuka a lokacin da ta tuno da mahaifinta da ya rasu kwanakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng