Tinubu Ya Sake Nada Shirgegen Mukami Mai Muhimmanci A Gwamnatinsa, an Fadi Sunan Matashin

Tinubu Ya Sake Nada Shirgegen Mukami Mai Muhimmanci A Gwamnatinsa, an Fadi Sunan Matashin

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon mukami a yau dinnan a bangaren ma su bukata ta musamman
  • Tinubu ya nada Muhammad Isa Abba a matsayin hadiminsa ta bangaren ma su bukata ta musamman
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya sha alwashin tafiya da kowa a gwamnatinsa don inganta rayuwar al'umma

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Tinubu ya amince da sabon nadi a bangaren ma su bukata ta musamman.

Tinubu ya nada Muhammad Abba Isa a matsayin hadiminsa a bangaren ma su bukata ta musamman.

Tinubu ya nada Abba a matsayin hadimi a bangaren ma su bukata ta musamman
Tinubu ya nada Abba mukamin hadiminsa. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Waye Tinubu ya nada sabon mukami?

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a shafin Facebook a yau Alhamis 9 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Tinubu ya amince da sabbin nade-nade 20, jerin sunaye

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TheCable ta tattaro cewa Isa na da kwarewa a bangarori da dama da su ka shafi mutane ma su bukata ta musamman.

Isa ya kammala digiri dinsa a bangaren gudanarwa da kuma digiri na biyu a jami'ar Maiduguri.

Wasu karin nade-nade Tinubu ya yi?

Wannan na daga cikin himmatuwar gwamnatin Tinubu na ganin ko wane bangare ya samu shiga don damawa da shi.

Tinubu ya bukaci Abba da ya samu hanyar damarmaki da zai inganta harkokin ma su bukata ta musamman.

Har ila yau, Tinubu ya yi sabbin nade-nade a bangaren Hukumar Kidaya ta kasa, NPC a jiya Laraba 8 ga watan Nuwamba.

Shugaban ya amince da nadin kwamishinoni a hukumar ta NPC har mutum 20 yayin da ake shirye-shiryen kidaya a kasar.

Hukumar ta shirya yin kidayar ce tun a mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kafin dakatar da shirin saboda wasu matsaloli.

Kara karanta wannan

Ana saura kwanaki 3 zaben gwamna, a karshe tsohon shugaban kasa ya bayyana wanda ya ke muradi

Tinubu ya nada Abdu a matsayin kwadinetan cibiyar lafiya

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya nada Dakta Abdu Mukhtar a matsayin kwadinetan cibiyar lafiya a ma'aikatar Tarayya.

Dakta Abdu zai kula da cibiyar ce don inganta harkar lafiya a kasar da take fama da matsaloli.

Tinubu ya yi wannan muhimmin nadi ne don samun hannun jari a cibiyar da kuma dakile fita kasar ketare jinya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel