Yan Arewa Na Murna Yayin da Tinubu Ya Nada Shirgegen Mukami a Harkar Lafiya, an Bayyana Matashin
- Shugaba Tinubu ya nada Dakta Abdu Mukhtar kwadinetan cibiyar lafiya ta fadar shugaban kasa a yammacin yau Talata
- Mukhtar kafin nadin nashi ya kasance darakta ne a ma’aikatar masana’antu da kasuwanci a bankin raya Nahiyar Afirka (AfDB)
- Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a yau Talata 7 ga watan Nuwamba a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi sabon nadi a ma’aikatar lafiya ta Tarayya a yammacin yau.
Tinubu ya nada Dakta Abdu Mukhtar a matsayin kwadinetan cibiyar lafiya ta ma'aikatar lafiya ta Tarayya.
Yaushe Tinubu ya nada Mukhtar mukamin?
Legit ta tattaro cewa Tinubu ya yi wannan nadin ne don samo hanyoyin zuba hannayen jari a harkar lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Talata 7 ga watan Nuwamba.
Ngelale ya ce wannan nadin an yi shi ne don inganta harkar lafiya a kasar da kuma dakile yawan fita neman lafiya kasashen ketare.
Waye Dakta Mukhtar da Tinubu ya nada?
Dakta Mukhtar ya kammala karatun digiti dinsa a Jami’ar Boston da kuma digiri dinsa na biyu a Cibiyar Kasuwanci ta Harvard, cewar TheCable.
Har ila yau, Mukhtar ya kuma yi karatun likitanci a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna.
Kafin wannan nadin nashi, Mukhtar darakta ne a ma’aikatar masana’antu da kasuwanci a bankin raya Nahiyar Afirka (AfDB).
Wannan mukami da aka bai wa Mukhtar na karakshin ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta Tarayya.
Tinubu ya nada shugabannin NCC, NITDA, NIPOST
A wani labarin, shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade a ma'aikatar sadarwa ta Tarayya.
Tinubu ya yi nadin ne a hukumomin NCC da NITDA da kuma NIPOST da ke karkashin ma'aikatar yada labarai ta Tarayya.
Sauran hukumomin sun hada da Hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta kasa (NIGCOMSAT) da Hukumar kare bayanan sirrin masu amfani da intanet ta kasa (NDPC).
Asali: Legit.ng