Tinubu Ya Yi Martani Ga Babatun Obi Kan Kotun Koli, Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Aka Ki Shi a Zabe

Tinubu Ya Yi Martani Ga Babatun Obi Kan Kotun Koli, Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Aka Ki Shi a Zabe

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bai wa Peter Obi muhimmiyar shawara bayan faduwa zabe a 2023
  • Tinubu ya shawarci Obi da ya kama wani layi na daban tun ya sha kaye a zabe kuma ‘yan kasar sun guje shi
  • Wannan na zuwa ne yayin da tsohon gwamnan Anambra ya yi martani a karon farko kan hukuncin kotun koli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya yi martani kan bayanan dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi kan hukuncin kotun koli.

Tinubu ya ce ya kamata yanzu Obi ya kama wani layi na daban ya bar babatu a harkokin siyasa bayan faduwa zabe.

Tinubu ya yi martani kan korafin Peter Obi a na hukuncin kotun koli
Tinubu ya fadi dalilin kin zaben Obi a Najeriya. Hoto: Bola Tinubu, Peter Obi.
Asali: Facebook

Wane martani Tinubu ya yi ga Obi?

Kara karanta wannan

Abin da ya sa ban halarci zaman yanke shari’a a Kotun Koli ba, Peter Obi ya yi martani

Yayin da ya ke martani kan hukuncin kotun koli, Obi ya ce hukuncin ya karya wa ‘yan Najeriya gwiwa inda ya ce zai sake tsayawa takara a shekarar 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Legit ta leko daga hadimin shugaban kan yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga.

Sanarwar da Bayo ya fitar a yau Litinin 6 ga watan Nuwamba ta bayyana cewa ‘yan Najeriya sun ki zaban Obi ne saboda barazana ne ga zaman lafiyar kasar.

Wane shawara Tinubu ya bai wa Obi?

Sanarwar ta ce:

“Shawarmu ga Mista Obi shi ne ya kama wani layi na daban don amfani da lokacinsa.
“Tun da mafi yawan ‘yan Najeriya sun guje shi saboda su na ganin bai cancanci ya mulki kasar Najeriya ba.
“Yan kasar sun ki Obi saboda ya kasance barazana ga zaman lafiyar kasar da ci gabanta.”

Kara karanta wannan

“Ina alfahari matuka”: Tinubu ya caccaki Atiku da Obi yayin da yake jawabi ga ministocinsa

Tinubu ya ce ya na mamaki ta yaya Obi zai ci zabe bayan ya haddasa gaba tsakanin Musulmai da Kiristoci wanda barazana ne ga zaman lafiya a kasar.

Obi ya yi martani kan hukuncin kotun koli

A wani labarin, dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi ya bayyana dalilin rashin halartar shari’ar kotun koli a watan jiya.

Obi ya bayyana cewa a wancan lokaci ya shirya fita kasar ketare don yin wasu ayyuka yayin da kotun ta sanar da ranar yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel