Abin da Ya Sa Ban Halarci Zaman Yanke Shari’a a Kotun Koli Ba, Peter Obi Ya Yi Martani

Abin da Ya Sa Ban Halarci Zaman Yanke Shari’a a Kotun Koli Ba, Peter Obi Ya Yi Martani

  • A karshe, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi ya yi martani kan hukuncin kotun koli da aka yanke
  • Obi ya bayyana dalilin rashin kasancewarshi yayin hukuncin da cewa ya yi tafiya zuwa kasar ketare don wasu ayyuka
  • Tsohon gwamnan Anambra ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a yau Litinin 6 ga watan Nuwamba a Abuja

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi ya bayyana dalilin da ya sa bai halarci shari’ar kotun koli ba.

Obi ya ce bai samu halartar kotun ba ne saboda wasu dalilai da su ka shafi ayyuka a kasashen waje babu shiri.

Kara karanta wannan

Kano: Bajiman lauyoyi sun yi watsa-watsa da hukuncin shari’ar Abba da Gawuna

Peter Obi ya yi martani kan hukuncin kotun koli a zaben shugaban kasa
Peter Obi ya yi martani kan hukuncin kotun koli. Hoto: Peter Obi.
Asali: Facebook

Mene Peter Obi ke cewa kan hukuncin kotu?

Tsohon gwamna jihar Anambra ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a yau Litinin 6 ga watan Nuwamba a Abuja, cewar BBC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Makwanni biyu da su ka wuce, na shirya tafiya kasar ketare babu shiri na samu labarin kotun koli ta saka ranar yanke hukunci.
“An riga an yanke hukuncin kamar yadda aka sanar a ranar 26 ga watan Oktoba a Abuja."

Mene dalilin yin martanin Obi?

“Jam’iyyarmu ta LP ta riga ta fitar da sanarwa kan wannan hukuncin kotun koli, a matsayi na wanda ya taba cin gajiyar hukuncin kotun koli, na yanke shawarar yin martani.”

Obi ya ce ya zama dole ya yi martani kan wannan hukunci kamar yadda mafi yawan ‘yan Najeriya su ka yi, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Babu maganar komawa Majalisa bayan Ministar Tinubu ta fado ta kai a Kotun zabe

A ranar 26 ga watan Oktoba, kotun koli ta yi fatali da kararrakin Peter Obi da Atiku Abubakar saboda rashin gamsassun hujjoji a tare da su, cewar Daily Trust.

Kotun koli ta yanke hukuncin zaben shugaban kasa

Awani labarin, Kotun koli da ke zamanta a birnin Tarayya Abuja ta yanke hukunci kan zaben shugaban kasa.

Kotun ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a zaben da aka gudanar a watan Faburairu.

Kotun ta kuma yi fatali da korafe-korafen Atiku Abubakar da takwaransa Peter Obi saboda rashin hujjoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel