Babban Labari: Gwamnatin Abba Ta Amince da Gina Gadoji da Manyan Ayyuka 15 a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci zaman majalisar SEC na takwas, watanni hudu bayan ya nada Kwamishinoni a Kano
- Majalisar zartarwa za ta bada kwangilolin ayyuka da za a aiwatar a kananan hukumomin Birni, Madobi, Kabo da sauransu
- Gwamnatin Abba za ta biya kudin sayen magunguna a asibitoci kuma za a gina dakin karatun da wuta ta cinye a makaranta
Kano - A karshen zaman majalisar zartarwa ta SEC da gwamnatin jihar Kano ta yi, an amince a yi wasu ayyukan more rayuwa da cigaba.
Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da matakin da aka dauka a shafinsa na Twitter a ranar Talata bayan zaman da ya gudana.
Wannan ne karo na takwas da majalisar zartarwa ta yi zama a karkashin Abba Kabir Yusuf.
Jerin ayyukan da Abba ya mince da su:
1. Ginin titin kasa da gadar sama a Dangundi a kan N15,974,357,204
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Ginin babbar gadar sama a Tal’udu a kan N15,455,507,265
3. Karin kudin aikin lambatun Jakara zuwa rafin Kwarin Gogau a kan N3,360,084,380
4. Ginin babban titin Kofar Waika-Unguwar Dabai-Yan Kuje a kan N1,579,755,966
5. Ginin gabar titin Unguwa Uku-Yan awaki-Limawa a kan N1,350,460,874
6. Karasa titin Kanye-Kabo-Dugabau a karamar hukumar Kabo a kan N820,262,071
7. Karasa bangaren titin Kofar Dawanau-Kwanar Madugu a kan hanyar Madobi a kan N802,695,617
8. Sake bada kwangilar gadojin tsallaka titi a wurare da-dama a fadin jihar N458,443,067
9. Gyaran wutan kan hanyoyi da na bada hannu a titi a kan N420,000,000
10. Biyan cikon kudin kwangilar gyaran titin Kwanar Kwankwaso a karamar Hukumar Madobi a kan N200,537,271
11. Ayyukan gyara Cibiyar gyaran hali ta Kiru a kan N107,658,976
12. Sayayyan kaya da magunguna a watan nan, domin bada kula a sassan hadura, agajin gaggawa, juna biyu da kananan yara a kan N53,654,223
13. Biyan kudin magunguna da sinadaran bincike da kayan aiki a asibitin yara na Hasiya Bayero N40,820,564
14. Biyan kason gwamnati wajen aikin rigakafin ‘Diphtheria; a kananan hukumomi 22 a kan N37,005,000
15. Sake gina dakin karatun da ya kone a makarantar koyon shari’a ta Aminu Kano a kan N56,763,475
Nasiru Gawuna v Abba Kabir Yusuf
A labarin shari'a, an ji Nasiru Gawuna ya dauko Ministan shari'a a gwamnatin Olusegun Obasanjo domin ya karbar masa mulkin Kano a Kotu.
Akinlolu Olujinmi, SAN da Wole Olanipekun, SAN suke karawa wajen daukaka karar shari’ar Kano inda ake neman karbe mulki daga hannun NNPP.
Asali: Legit.ng