Tsohon Gwamnan APC Ya Yi Rashin Nasara Bayan Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Sanata
- Kotun ɗaukaka ƙara da ke Legas ta yi watsi da ƙarar tsohon gwamnan Jihar Cross Rivers, Ben Ayade, wanda ya ƙalubalanci nasarar Jarigbe Jarigbe a zaɓen Sanatan Cross Rivers ta Arewa
- Kotun ta tabbatar da Jarigbe ɗan jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben sannan ta umurci Ayade wanda ya tsaya takara a jam’iyyar APC da ya biya N500,000 ga Sanatan mai ci
- Wannan hukuncin ya biyo bayan rashin nasarar Ayade a zaɓen watan Fabrairu, inda Jarigbe ya samu ƙuri’u 76,145 fiye da ƙuri’u 56,595 na Ayade
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
Jihar Legas - Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Legas ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan jihar Cross Rivers, Ben Ayade ya shigar na ƙalubalantar nasarar Jarigbe Jarigbe a zaben sanatan Cross Rivers ta Arewa a 2023.
Kotun a ranar Asabar, 4 ga watan Nuwamba, ta tabbatar da Jarigbe na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Kotun ta kuma umarci tsohon gwamnan da ya biya N500,000 ga Sanata mai ci, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaɓen 2023: Yadda Ayade ya yi rashin nasara
Idan ba ku manta ba dai, Ayade ya sha kaye a zaɓen watan Fabrairu a hannun Sanata Jarigbe.
Jarigbe ya samu ƙuri’u 76,145 inda ya doke Ayade wanda shi ma tsohon Sanata ne inda ya samu ƙuri’u 56,595.
Saboda rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen, tsohon gwamnan ya shigar da ƙara a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun jihar Cross Rivers da ke zamanta a birnin Calabar, babban birnin jihar.
Sai dai, kotun ta tabbatar da Jarigbe a matsayin wanda ya yi nasara tare da yin watsi da ƙarar Ayade saboda rashin cancantar ta.
Ƙoƙarin da ya yi na ganin an yanke masa hukunci mai kyau a kotun ɗaukaka ƙara ya ci tura domin kotun ta yi watsi da ƙarar.
Jarigbe ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai har sau biyu. An zabe shi a matsayin sanata a zaɓen cike gurbi a watan Satumban 2021 bayan rasuwar Dr Rose Okoh.
Kotun Daukaka Ƙara Ta Sanya Ranar Fara Sauraron Shari'ar Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kotun ɗaukaka ƙara ta sanya ranar fara sauraron ƙarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya ɗaukaka kan zaɓen gwamnan jihar.
Kotun za ta fara sauraron ƙarar a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba kan ƙarar da Abba ya ɗaukaka yana ƙalubalantar nasarar Nasiru Gawuna a kotun zaɓe.
Asali: Legit.ng