Gwamna Ayade Na Jahar Kuros Riba Ya Yi Sauye-Sauye a Majalisarsa Watanni Kafin Barinsa Mulki

Gwamna Ayade Na Jahar Kuros Riba Ya Yi Sauye-Sauye a Majalisarsa Watanni Kafin Barinsa Mulki

  • Gwamna Ben Ayade ya kafa tarihi a Kuros Riba ta hanyar nada Musulmi na farko da ba dan jihar ba a matsayin kwamishina
  • Adamu Uba Musa daga jihar Kano shine sabon kwamishinan harkokin gwamnati a jihar ta kudu
  • Wani babban dan jarida a jihar ya ce wannan yumkuri na gwamnan zai kara hada kan jama’a da zaman lafiya a jihar

Cross River - Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba ya sauya fasalin majalisarsa sannan ya rantsar da dan arewa da wasu 12 a matsayin kwamishinoni.

Daya daga cikin sabbin mutanen da aka nada shine Adamu Musa daga jihar Kano. Shine sabon kwamishinan harkokin gwamnati a jihar ta kudu maso kudu.

Ben Ayade
Gwamna Ayade Na Jahar Kuros Riba Ya Yi Sauye-Sauye a Majalisarsa Watanni Kafin Barinsa Mulki Hoto: @senatorbenayade
Asali: Twitter

Wani rahoton The Cable ya bayyana cewa an nada Eric Anderson, tsohon kwamishinan al’adu da yawon bude ido a matsayin kwamishinan labarai.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Dauki Sabbin Alkawurra a Bangaren Ilimi, Ya Bude Shafin Tallafin Kamfen 2023

Dr Janet Ekpenyon, tsohuwar Darakta Janar ta hukumar ci gaban asibitocin jihar ta zama kwamishinar lafiya, rahoton Sahara Reporters.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ga sabbin kwamishinonin a Calabar, babban birnin jihar a ranar Talata,10ga watan Janairu, Gwamna Ayade ya ce:

“Zuwanku ba bisa hasari bane. An duba an darje wajen zabenku saboda mutunci da cancantarku don bayar da gudunmawarku a wannan gwamnati namu.
“An yankarwa kowannenku aikinsa, Ina tsammanin cewa za ku saka jahar mu ta zamo mai alfahari.”

Musa ne Musulmi na farko da ba dan jaha ba da ke cin mukamin kwamishina a Kuros Riba

Da yake karin haske kan nadin Musa, dan jarida mazaunin Calabar, babban birnin jihar Cross River, John Ekpeyong ya fada ma Legit.ng cewa sabon kwamishinan shine Musulmi na farko da ba dan jaha ba da ke rike wannan mukamin.

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

Ekpenyong wanda ke aiki a gidan radiyon jihar ya ce:

“Mutanen jihar sun samu labarin nadin da ra’ayoyi mabanbanta. Yayin da wasu ke ganin zai kara hadin kai, wasu na ganin gwamnan na shigo da ra’ayin yan waje.
“Ni a nawa tunanin, Ina ganin babu wani laifi a kan wannan. A arewa, Muna da yan kudu da dama da ke rike da mukamai daban daban.
“Magana ta Gaskiya, a wannan gabar, rike irin wannan mukamai bai kamata ayi la’akari da inda mutum ya fito ba, kamata ya yi a duba cancantar mutumin Da Kuka yadda ya bayar da gudunmawa ga wannan al’umma kuma ina ganin wannan ne abun da Gwamna Ayade ya duba.”

Alan waka ya janye daga takarar kujerar dan majalisa

A wani labarin kuma, shahararren mawakin kannywood, Aminu Ladan wanda aka fi sani da Alan waka ya fita daga tseren neman kujerar dan majalisar wakilai na jahar kano.

Ala ya ce ya janye ne saboda ba shi da wata shaida da ke nuna lallai shi din dan takara ne har zuwa yanzu da zabe ke kara gabatowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel