Kungiyar Arewa Ta Yi Barazanar Dakatar Da Kai Kayan Abinci Kudancin Najeriya
- Kungiyar Arewa ta yi barazanar fara zanga-zangar luma tare da dakatar da kai kayan abinci Kudu ma damar Sunday Igboho ya kori Fulani daga kasar yarbawa
- Haka zalika, kungiyar ta ba gwamnatin tarayya wa'adin makonni hudu, ta biya haddin mutanen Arewa da aka kashe a garuruwan Kudu
- A cewar kungiyar, idan har aka gaza biyan bukatun ta, kuma aka kori Fulani daga Kudu, to ita ma za ta fatattaki yarbawa da ke zaune a garuruwan Arewa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Arewa - Kungiyar 'Northern Consensus Movement (NCM), mai rajin kare muradun 'yan Arewa, ta sha alwashin dakatar da kai kayan abinci daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya.
Kungiyar ta yi wannan barazanar ne biyo bayan wani wa'adi da dan rajin kare martabar yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya ba al'ummar fulani da su fice daga kasar yarbawa cikin kwanaki goma ko ya dauki mataki.
Kungiyar ta ce za ta yi duk mai yiyuwa na dakatar da wannan kudirin na Igboho, amma idan wannan barazanar ta su ba ta ci ba, to za su dauki matakin fatattakar duk wasu yarbawa da ke zaune a garuruwan Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za mu kori yarbawa daga garuruwan Arewa - Kungiyar NCM
Shugaban kungiyar, Awwal Aliyu, ya yi wannan gargadin a ranar Alhamis a wani taron manema labarai.
Bidiyon taron, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, ya mamaye kafofin watsa labarai da sada zumunta. A cikin bidiyon, anji Aliyu yana cewa:
"Ba a jima da sako Sunday Igboho daga gidan gyaran hali ba, amma har ya fitar da sanarwar barazana ga al'ummar fulani da ke zaune a garuruwan yarbawa, tare da ba su umurnin fice wa daga yankins cikin kwanaki goma."
"A wannan karon, kungiyar mu ta 'Northern Consensus Movement' za ta yi duk mai yiyuwa na ganin ta dakatar da hakan daga faruwa, amma idan ya ki ji, za mu dauki matakin fatattakar yarbawa daga garuruwan Arewa, in yaso, kowa ya zauna a kasar sa."
Kungiyar Arewa ta ba da wa'adin kwana bakwai ko ta fara zanga-zanga
Kungiyar ta kuma bukaci a biya Arewa haddin mutanenta da aka kashe ko aka lalata masu dukiya a rikicin ENDSARs, kasuwar Shasha-Akinyele da kuma IPOB/ESN, jaridar Daily Times ta ruwaito.
Ta yi nuni da cewa gwamnatin da ta shude da gwamnati mai ci a yanzu a kasar sun yi biris da wannan bukatar ta su, don haka a yanzu suka bayar da wa'adin makonni hudu ga gwamnatin ta cika wannan sharadi, rashin yin hakan zai sa kungiyar ta gudanar da zanga-zanga a fadin kasar, tare da dakatar da kai kayan abinci zuwa Kudu.
Muna kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya yi mai yiyuwa akan wannan bukatar ta mu. Mun ba da wa'adin makonni hudu, idan babu abinda aka yi, to za mu gudanar da zanga-zangar lumana, wanda hakan zai jawo dakatar da kai kayan abinci daga Arewa zuwa Kudu.
Tun kafin a zabe shi a matsayin shugaban kasa muka aika masa da wannan bukatar, haka zalika mun sanar da hukumomin tsaro, gwamnoni 19 na jihohin Arewa, tsoffin gwamnoni da tsohon shugaban kasa.
- Awwal Aliyu
Kungiyar ta kuma yi kira ga babbar kungiyar kabilar yarbawa ta Afenifere, da ta gargadi Sunday Igboho, ya shiga tai-tayinsa akan matakin da ya ke shirin dauka.
Gara mu yi asarar kayan da mu kai Kudu - Yan kasuwa a Arewa
Kungiyar gamayya ta masu siyar da kayan abinci tare da masu siyar da shanu ta Najeriya (AUFCDN) ta ce ta gwammace kayan abinci su lalace da ta ci gaba da lamuntar harin da ake kai wa mambobinta na Kudu.
Asali: Legit.ng