Gara mu yi asarar kayan, 'Yan kasuwan arewa sun yi martani kan hana kudu kayan abinci
- Kungiyar masu siyar da kayan abinci da shanu ta arewa tace gara kayanta su lalace da su kai kudu
- Kamar yadda jami'in kungiyar ya sanar, asarar dukiya ta fi asarar rayuka kamar yadda ake kashesu a kudu
- Ya ce har sai 'yan kudu sun koyi dena kashe mutanensu sannan ne za su samu abinci da nama daga arewa
Kungiyar gamayya ta masu siyar da kayan abinci tare da masu siyar da shanu ta Najeriya (AUFCDN) ta ce ta gwammace kayan abinci su lalace da ta cigaba da lamuntar harin da ake kaiwa mambobinta na kudu.
Awwalu Aliyu, jami'in kungiyar wanda ya tattauna da TheCable a Kano ranar Talata, ya ce wannan hukuncin ba na saka 'yan kudu a yunwa bane, amma na nuna rashin jin dadi da yadda ake kaiwa mambobinsu hari ne.
Aliyu ya zargi cewa wasu daga cikin mambobinsu da gangan aka kashesu tare da barnatar musu da dukiyoyinsu ballantana yayin zanga-zangar EndSARS da kuma rikicin kasuwar Shasha a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
KU KARANTA: Da duminsa: Sojoji sun mamaye Dikwa, sun fatattaki mayakan Boko Haram
A yayin da aka tambayesa ko wannan lamarin bai shafi mambobinsu ba ta yadda aka rufe kayan a Jebba, jihar Neja, kuma akwai yuwuwar su lalace tare da asara, Aliyu yace: "Gara a rasa kayan da a rasa rayuka."
"Kuna batun asarar kaya, wanne yafi tsakaninsu da rayuka? Rasa kadara ya fi rasa rayuwar mutum daya.
"Mun fi son haka kuma mutanenmu za su fi son a rasa kayan nan da a cigaba da rasa rayuka. Idan kana da rai, za ka iya shuka duk abinda kake so kuma ka kiwata shanun. Amma idan ka mutu, komai naka ya tsaya."
KU KARANTA: Babu sasanci tsakaninmu da 'yan bindiga, Gwamnatin Kaduna ta jaddada
A wani labari na daban, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya ce akwai shirin cewa 'yan ta'adda za su iya sace wasu jama'an domin su tozarta gwamnatin tarayya.
Ministan ya sanar da hakan ne a ranar Litinin bayan ganawa da yayi da shugaban kasa Muuhammadu Buhari, The Cable ta wallafa.
Tun a farko ministan ya mika alkawarin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yace sace yaran makarantar sakandare na Jangebe zai zama na karshe a kasar nan.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng