Yarbawa dake zaune a arewa sun nesanta kansu daga neman jumhuriyar Oduduwa

Yarbawa dake zaune a arewa sun nesanta kansu daga neman jumhuriyar Oduduwa

- Kungiyar Yarbawa na Yoruba Liberation Command ta yi kira ga yankinsu das u nemi jumhuriyar Oduduwa, wata sabuwar kasa

- Alúmmaan Yarbawa dake zaune a jihohin arewa 19 dake kasar sun nesanta kansu daga wannan fafutukar

- Sun kuma karyata cewan a nemi shawarar su kafin a sanar da fafutukar jumhuriyyar Oduduwa

Alúmman Yarbawa dake zaune a yankin arewacin Najeriya sun gargadi wadanda ke fafutukar neman jumhuriyar Oduduwa cewa su babu hannunsu a ciki.

Karkashin jagorancin Dr Jimoh Aiyelangbe, mukadashin shugaban kungiyar, Yarbawa dake zaune a jihohi 19 na arewacin kasar harda Abuja, sun nesanta kansu daga fafutukar.

Da yake Magana a Kano don maida martini ga kira da kungiyar Yoruba Liberation Command (YOLICOM), Aiyelangbe yace baá taba tuntubar sa a kan abu makamancin wannan ba.

Yarbawa dake zaune a arewa sun nesanta kansu daga neman jumhuriyar Oduduwa
Yarbawa dake zaune a arewa sun nesanta kansu daga neman jumhuriyar Oduduwa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa bayan masu fafutukar neman Biyafara, wata kungiya daga kudu maso yamma, Yoruba Liberation Command (YOLICOM) ta kaddamar da son rabewa daga Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari za ta ziyarci jihar Imo a gobe LarabaAisha Buhari za ta ziyarci jihar Imo a gobe Laraba

Kungiyar wacce tayi kaddamarwan a jihar Lagas a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, tace zata kafa kasar Oduduwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel