"Tinubu Ya Taya Arewa, Sun Sayar, Ya Biya Lakadan”, Farfesa Usman Yusuf Ya Yi Zazzafan Martani

"Tinubu Ya Taya Arewa, Sun Sayar, Ya Biya Lakadan”, Farfesa Usman Yusuf Ya Yi Zazzafan Martani

  • Tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf ya yi tir da salon nade-naden mukaman shugaban kasa Bola Tinubu
  • Farfesa Yusuf ya ce Tinubu yana nuna fifiko ga kabilarsa wajen nade-naden mukamai a gwamnatinsa
  • Yusuf ya ce an yaudari arewa da tikitin Muslim-Muslim har suka kai Tinubu kan kujerar shugabanci

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon babban sakataren hukumar kula da inshoran lafiya, Farfesa Usman Yusuf, ya zargi gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da nuna fifiko wajen rabon mukamai.

Kamar yadda dattijon arewan ya bayyana a cikin wata hira da aka yi da shi, ya ce ana nuna fifiko ga wani bangare na wannan kasar.

Farfesa Usman Yusuf ya zargi Tinubu da nuna fifiko ga ka
"Tinubu Ya Taya Arewa, Sun Sayar, Ya Biya Lakadan”, Farfesa Usman Yusuf Ya Yi Zazzafan Martani Hoto: @SaharaReporters
Asali: Twitter

An yaudari arewa da Muslim-Muslim, Farfesa Yusuf

Kara karanta wannan

“Ina alfahari matuka”: Tinubu ya caccaki Atiku da Obi yayin da yake jawabi ga ministocinsa

A cewarsa, hakan ya kasance ne duk da cewar arewa ce ta yi ruwa ta yi makadiya wajen ganin Shugaba Tinubu ya hau kujerar shugabancin kasar, cewa an yaudare su da tikitin Muslim-Muslim.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce shakka babu Tinubu ya siya arewa kuma ya biya lakadan ba ajalan ba.

Farfesa Yusuf ya ce:

"Ni dai abun da nake cewa shine shugaban kasa ya siya kuma arewa ta siyar kuma ya biya lakadan, shiyasa yanzu yake yin abun da ya ga dama. Saboda haka kun siyar ya siya, sauran bayani kuma da fashin baki jama’a su gane.”

Da aka tambaye shi game da abun da yake nufi da an siyar ya siya Farfesan ya ce:

“Toh Arewa ta zabe shi ko? Aka kawowa arewa wannan yaudarar Muslim-Muslim , malamai aka yaudari jama’a Muslim-Muslim, toh yanzu sai ka yi zaton ko Lagas bai ci ba arewa ta zabe shi amma a zo wurin nade-nade sai bangaran shi kawai, kuma ba bangare ba kabilar shi saboda haka wannan laifin arewa ne.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da kujerarsa ke tangal-tangal ya nemi afuwar talakawan jiharsa kan abu 1 da ya faru

“Ina yan arewan? Kowa ya yi shiru don ya riga ya siya kuma an sayar kuma ya biya lakadan. Kwarai arewa an riga an yi cinikinta. Arewa dai ga shi nan an zo malamai sun sai da mana Muslim-Musulim ga shi mu ke wahala, ko ba wahala ake yi ba?”

Kan cewa Tinubu ya gaji wahalar da ake ciki ne daga gwamnatin Muhammadu Buhari, dattijon arewan ya ce:

“Kuma ba gaskiya bane ana cewa wai shugaban kasa Muhammadu Buhari abun da ya yi kenan wannan ba gaskiya bane. Shugaba Buhari bai bar bangare daya cikin shida ba kawai, bai ba kabila day aba cikin shida a cikin kabilun da ke Najeriya ba kuma abun da ke faruwa kenan a wannan gwamnati. Kabila daya cikin kabilun da ke Najeriya, bangare daya cikin bangare shida da ke Najeriya su ake fifitawa.”

Legit Hausa ta zanta da wani dan arewa don jin ta bakinsa kan wannan batu.

Kara karanta wannan

Murna yayin da Faransa za ta dawo da makudan kudin da Abacha ya sace

Mallam Abubakar Sani ya ce:

"Ni dai ban ga laifin shugaban kasa Tinubu ba kan wannan nade-nade da ya yi kuma yake kan yi. Kowa ya sai rariya ya san za ta zub da ruwa, kuma Hausawa sun ce so sone amma son kai ya fi. Ai muma an yi a arewa mun gani. A zamanin Buhari shima ya nada yan arewa kan mukamai da dama sai dai ana iya cewa bai kai na Tinubu.
"A ganina babban abun dubawa shine shin wadanda aka ba mukaman za su kawo sauyi a kasar, za su yiwa kowa adalci ba tare da la'akari da waye dan yankinsu ba, ba wai a tsaya ana maganar an fifita wata kabila wajen rabon mukamai ba. Mu dai abun da muke so a matsayinmu na yan arewa shine a inganta mana tsaro ta yadda za mu yi bacci da idanunmu a rufe, yayanmu su samu ilimi sannan kori talauci daga yankinmu kawai shine batu."

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

Tinubu ya yi martani ga furucin Atiku

A wani labarin, Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi martani ga taron manema labarai na Atiku Abubakar, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, cewa a karshe tsohon mataimakin shugaban kasar ya gano muryarsa.

Tinubu ya ce Atiku ya karyata shi a inda ya yi tunanin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar zai nuna dattako ta hanyar sako Najeriya a gaba, amma sai aka samu akasin haka a taron manema labaran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng