Tsohon Minista Amaechi Ya Yi Magana Bayan Nasarar Shugaba Tinubu a Kotun Koli

Tsohon Minista Amaechi Ya Yi Magana Bayan Nasarar Shugaba Tinubu a Kotun Koli

  • Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya kawo ƙarshen shirun da ya kwashe tsawon lokaci yana yi
  • Wannan dai na zuwa ne jim kaɗan bayan da kotun ƙoli ta tabbatar da Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa na 2023
  • A wani martani da ya yi cikin shaguɓe, Amaechi ya ce babu wani abu da ya yi saura a Najeriya, kuma ƴan Najeriya ba sa mayar da martani ko da sun san gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi magana ƙasa da sa’o’i 24 bayan kotun ƙoli ta tabbatar da Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa na 2023.

Da yake magana a wani taron a Abuja a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoba, Amaechi ya bayyana cewa kafafen yaɗa labarai da dama sun tuntube shi domin tattaunawa kan batutuwa da dama amma sai ya zaɓi ya ƙi yin hakan.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Fitaccen Lauyan Najeriya Ya Yi Bayani Kan Nasarar da Tinubu Ya Samu a Kotun Ƙoli

Amaechi ya yi magana a karon farko
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya magantu bayan nasarar Tinubu a kotun koli Hoto: Rt Hon Chibuike R Amaechi
Asali: Facebook

Ya kuma ce, "Ba wani sabon abu da za a ce" saboda ƴan Najeriya ba sa mayar da martani ga batutuwa.

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Menene sabon abin da za a ce? Ƴan Najeriya ba su yin martani kan komai. Kamar yadda wani ɗan siyasa ya ce muku shi ba ɓarawo ba ne? Gaya min wani ɗan siyasa ɗaya wanda ba ɓarawo ba ne? Wane ɗan siyaya ne ya gaya muku bai yi takardun jabu ba? Wane ɗan siyasa ya gaya muku cewa ya je jami'a? Wane ɗan siyasa ne ya ce muku ya yi NYSC? Wane ɗan siyane ne ya ce muku yana da satifiket? Ƴan Najeriya sun sani kuma duk da haka suka zaɓe su, don haka menene matsalarku?

Ameachi ya koka da yadda ƴan Najeriya ke nuna halin ko in kula

Ya kuma ƙara da cewa babu wani abu da ke damun ƴan Najeriya, ko da kuwa ta fuskar gaskiya, kuma ba zai ɓata lokacinsa ba wajen tattaunawa da kuma yin magana kan wadannan batutuwa ba.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Bayyana a Karon Farko Bayan Ya Sha Kashi Hannun Tinubu a Kotun Ƙoli

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya kuma bayyana irin matsalolin da ya sha tun daga gwamnatin Goodluck Jonathan zuwa gwamnatin Muhammadu Buhari.

"Idan aka kashe ni me zai faru? Ba komai! To, me na zaba? Na zaɓi in zauna a gidana na yi shiru. Na zaɓi kada in ƙara magana saboda babu abin da za a ce domin ƴan Najeriya ba za su yi komai ba." A cewarsa.

Da yake kwatanta irin mawuyacin halin da Najeriya ke ciki, Amaechi ya bayyana cewa hukumomi na iya ɗaukar mutumin da ba shi da laifi a kulle shi hakanan kawai, kuma ƴan Najeriya ba za su ce komai a kai ba

"Babban tsoron da nake da shi shine na samu kai na a gidan yari ba tare da aikata komai ba, kuma za ka iya tsintar kan ka a gidan yari ba tare da yin komai ba." A cewarsa.

Amaechi Ya Zargi Hadiza Bala Usman

Kara karanta wannan

An Shawarci Atiku da Obi Kan Abin da Ya Kamata Su Yi Bayan Kotun Koli Ta Tabbatar da Nasarar Tinubu

A wani labarin kuma, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya zargi tsohuwar shugabar hukumar NPA, Hadiza Bala Usman da tafka ƙarya a littafin da ta rubuta.

A littafinta, tsohon Ministan ya ce tsohuwar shugabar ta NPA ba ta yi bayanin gaskiyar abubuwan da su ka sa aka kore ta daga ofis ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel