Amaechi: Tsohon Ministan Ya Fadi Ainihin Dalilin Korar Hadiza Bala Usman Daga NPA

Amaechi: Tsohon Ministan Ya Fadi Ainihin Dalilin Korar Hadiza Bala Usman Daga NPA

  • Rotimi Amaechi ya yi martani na farko a game da abubuwan da Hadiza Bala Usman ta fada a littafin da ta rubuta
  • Tsohon Ministan ya ce tsohuwar shugabar ta NPA ta lafta karyayyaki iri-iri, ya fadi dalilin korar ta daga hukumar NPA
  • Amaechi ya zargi Hadiza Bala Usman da sabawa doka da rashin bin ka’idojin aiki, yake cewa saboda haka aka tsige ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya kan kawo labarai na Hausa musamman na siyasa, addini, wasanni da al’ada

Lagos - Rotimi Amaechi wanda ya rike Ministan sufuri a gwamnatin Muhammadu Buhari, ya maida martani ga Hadiza Bala Usman.

Hadiza Bala Usman ta yi rubutu game da abubuwan da su ka faru da ta ke NPA, Daily Trust ta ce Rotimi Amaechi ya waiwayi littafin na ta.

Kara karanta wannan

Rarara: Tsohon Hadimi Ya Mayar Wa Mawaki Raddi Mai Zafi Saboda Caccakar Mulkin Buhari

Amaechi ya yi jawabi ne a wajen wata lacca da aka shirya a garin Legas game da shugabanci, kishin kasa da halin da Najeriya ke ciki.

Hadiza Bala Usman
Tsohuwar shugabar NPA Hoto: Hadiza Bala Usman
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadiza Bala Usman ta boye gaskiya?

A littafinta, tsohon Ministan ya ce tsohuwar shugabar ta NPA ba ta yi bayanin gaskiyar abubuwan da su ka sa aka kore ta daga ofis ba.

Rahoton ya ce babban ‘dan siyasar ya karyata zargin da ake yi masa tun daga cewa an yi waje da ita ne saboda ta daina ba shi kyauttuka.

A cewar Amaechi, tun da ya zama Minista ya bukaci Hadiza Bala Usman ta daina kawo masa kyauta kamar yadda ta saba ranar haihuwarsa.

Amaechi ya ce Hadiza ta sabawa doka

Doka ta ba shugabar NPA damar amincewa a batar da N2.5m ne kawai, Mista Amaechi ya ce Hadiza Usman ta bada kwangila har ta N2.4bn.

Kara karanta wannan

“Wike Na Da Laifinsa”: MURIC Ta Goyi Bayan Gumi Yayin Da Ya Kira Ministan Abuja ‘Shaidani’

Bayan haka, jagoran na APC da aka daina jin duriyarsa bayan yakin zaben 2023 ya ce binciken BPE ya gano an kara kudin aikin da N58m.

"An yi ta muhawara watanni shida da su ka wuce a kan ko in maida martani ko ka da in yi, zan yi martani duk da 90% sun ce in yi shiru.
Karyayyakin sun yi yawa. Alal misali, ta yi ikirarin kwamiti bai gayyace ta ba. Har wajen shugaban kasa na zo da takardar da aka tsige ta."

- Rotimi Amaechi

"An kawo kabilanci a mulki" - Amaechi

Sai an dauki mataki a FEC, Amaechi ya ce sai Hadiza Usman ta canza da sunan kishin kasa, ya kuma zargi shugabanninyau da kabilanci.

Tsohon gwamnan ya ce shugaban kasa na karshe da aka yi mai kishin Najeriya shi ne Olusegun Obasanjo, ya ce yanzu ana kabilanci a mulki.

Rarara ya yi kaca-kaca da Buhari

Kara karanta wannan

Wuta Ta Kunno a APC, Ana Rikici Tsakanin Minista da Shugaban Majalisar Tarayya

Ana da labari cewa Dauda Kahutu Rarara ya ce kyau idan za a kafa gwamnati, ya kawo sunayen Ministoci akalla biyu saboda ya wahala.

Mawakin siyasar ya na ganin babu wanda ya taimaki APC irinsa sai wasu tsofaffin Gwamnon; Aminu Masari da kuma Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel