Obasanjo Ya Ba Tinubu Shawarwarin Da Za Su Taimaka Wajen Dawo da Darajar Naira

Obasanjo Ya Ba Tinubu Shawarwarin Da Za Su Taimaka Wajen Dawo da Darajar Naira

  • Olusegun Obasanjo ya ba Gwamnatin da Bola Ahmed Tinubu ya ke jagoranta shawarar yadda za a farfado da tattalin arziki
  • Tsohon Shugaban Kasar ya bukaci a haramta shigo da kaya daga kasar Sin domin a iya inganta masana’antun da ake da su a nan
  • Idan aka dauki wannan matakin, Obasanjo ya ce mutane za su samu ayyukan yi, kuma tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya kan kawo labarai na Hausa musamman na siyasa, addini, wasanni da al’ada

Ogun - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta haramta shigo da kayayyki daga kasashen waje.

Olusegun Obasanjo ya na so a daina kawo tufafi da kayan Sin zuwa Najeriya domin a inganta tattalin arzikin kasa, labarin ya zo a jaridar Tribune.

Dattijon ya zargi kasar Sin da kashe harkar kasuwan yadi a Najeriya, a sakamakon haka Naira ta na rasa darajar ta a sahun sauran kudi.

Kara karanta wannan

Za a Biya Nnamdi Kanu Naira Biliyan 8 Bayan Kotu Ta Soke Haramcin Kungiyar IPOB

Obasanjo
Bola Tinubu da Olusegun Obasanjo Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obasanjo ya na so a inganta tattalin arziki

Idan ana so a farfado da tattalin arziki kuma a samar da ayyukan yi a gida, Olusegun Obasanjo ya ce dole a ceci kayayyakin da ake yi a nan.

Obasanjo wanda ya yi mulki sau biyu ya yi wannan kira ne jawabin da ya gabatar a garin Abeokuta a wani taro da aka shirya a kan kasuwanci.

Solteque Nigeria Ltd ya shirya taron da aka gayyato manya da jami’an gwamnati irinsu Realtor Babatunde Adeyemo da Mrs Oluwatosin Oloko.

An kashe 'yan kasuwan Kano da Kaduna

Obasanjo ya ce kamfanonin da su ka saba samar da tufafi a Kano, Kaduna da Ekiti sun mutu. Shawararsa ta yi kama da ta Kingsley Mogalu.

Vanguard ta ce Obasanjo ya nemi gwamnatin da Bola Tinubu ya ke jagoranta ta farfado da tattalin arziki ta hanyar bunkasa masana’antu.

Kara karanta wannan

Rarara: Tsohon Hadimi Ya Mayar Wa Mawaki Raddi Mai Zafi Saboda Caccakar Mulkin Buhari

Baya ga haka, tsohon sojan ya yi kira a samar da cibiyar horas da mutane da za su koyi irin wadannan ayyuka kuma a rika ba su takardar shaida.

Za a karya masu noman shinka

"Gwamnati ta cire takunkumin shigo da shinkafa da Dala, masu noman shinkafa su shirya domin za a kawo shinkafa mafi araha daga Thailand.
Gwamnatin Thailand ta kashe makudan kudi a harkar noman shinkafa domin kawo su Najeriya saboda a lalata shinkafar gida."

Atiku Abubakar da Peter Obi sun fadi a kotu

Kun ji labari Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar ya gabatar da sababbin hujjoji kan Bola Tinubu a kotun koli, amma Alkalai ba su karba ba.

Peter Obi da ya yi takara a LP ya nemi a rusa nasarar APC, a damka masa shubancin Najeriya, shi ma bai yi nasara a kotun na Allah ya isa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng