An Tsinci Gawar Wata Dalibar Najeriya Da Ta Mutu a Dakin Saurayi

An Tsinci Gawar Wata Dalibar Najeriya Da Ta Mutu a Dakin Saurayi

  • An tsinci gawar wata dalibar mataki na uku a jami'ar UNIPORT, Otuene Justina Nkang, a dakin saurayinta
  • Wanda ake zargin, wanda ke zaune a wani babban yanki na Port-Harcourt ya kashe Nkang sannan ya yanyanka sassan jikinta
  • Yan banga ne suka cafke wanda ake zargin a lokacin da yake kokarin jefa gawar da ta rube a wani bola

Jihar Rivers - An gano gawar wata daliba a mataki na uku a jami'ar Port Harcourt (UNIPORT), Otuene Justina Nkang, a dakin saurayinta da ke babban birnin jihar Ribas.

An ayyana batan Nkang kwanaki hudu da suka gabata bayan ta bar wajen aikinta, inda take koyon horo a wani asibiti mai zaman kansa a Port Harcourt.

Saurayi ya kashe budurwa don kudin jini
Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Aka Tsinci Gawar Dalibar Da Ta Bata a Dakin Saurayi Hoto: East9ja
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, wata majiya ta ce saurayin Nkang ya kashe ta sannan ya yanke nononta, ido da wasu sassan jiki.

Kara karanta wannan

Uba Ya Shiryawa Diyarsa Kasaitaccen Biki Na Dawowarta Gida Bayan Mutuwar Aurenta, Bidiyon Ya Yadu

Yadda aka kama saurayi da gawar budurwarsa

An tattaro cewa marigayiyar ta bar wajen aikinta domin ziyartan saurayinta a wani babban yanki da ke garin Port Harcourt.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce yan banga da ke yankin sun cafke wanda ake zargin ne a lokacin da yake kokarin jefa gawar da ta rube a wani bola.

Majiyar ta ce:

“An ba da rahoton batan Otuene Justina Nkang kwanaki hudu da suka gabata. Ita daliba ce a matakin 300l a jami'ar Uniport amma abin takaici, saurayinta ya kashe ta inda ya yi yunkurin jefar da gawarta a yammacin yau (Laraba) amma aka kama shi. An mika wanda ake zargin ga yan sanda."

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, an kama wanda ake zargin, Collins, wanda ke zaune a kan gida mai lamba 15, NTA Road, Port Harcourt, ne bayan jami’an tsaron unguwarsu sun gano sassan jikin Justina da aka daddatsa a cikin buhu mai jini.

Kara karanta wannan

Hanya 1 Za a Bi Domin Hana Farashin Dala Tashi - Tsohon Mataimakin Sanusi a CBN

Da take martani kan lamarin, kakain yan sanda, SP Grace Iringe Koko, ta ce kwamishinan yan sanda, Policarp Emeka Nwaonyi, zai yi jawabi ga manema labarai kan lamarin a yau Alhamis.

An gano gawar dalibar FUOYE

A wani labari makamancin wannan, mun kawo a baya cewa an tsinci gawar wata dalibar jami'ar tarayya ta Oye Ekiti (FUOYE), Atanda Modupe Deborah.

An ayyana batan Atanda, dalibar sashin kula da jinya wacce ke a mataki na biyu bayan ta fita zuwa aji don yin karatu a daren ranar Litinin, 4 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng