Saurayi ya kashe budurwarsa bayan an bashi N2m domin amfani da ita wurin tsafi
- Wani matashi mai suna Yusuf ya shiga hannun 'yan sandan jihar Legas bayan kama shi da aka yi da laifin kisan kai
- Budurwa mai suna Toluwase Kembi ta je yi wa wani saurayinta girki, amma bata dawo ba a watan Augustan 2020
- Bayan damke matashin, ya ce miliyan 2 aka bashi kuma ya kasheta tare da bada namanta domin yin tsafi da shi
Toluwase Kembi budurwa ce mai shekaru 20 da ke karantar fannin kasuwanci a makarantar gaba da sakandare ta Ilaro da ke jihar Ogun.
An tabbatar da cewa ta mutu bayan saurayinta da take zuwa wurinsa a yankin Ikorodu ta jihar Legas ya kasheta.
A makonni kadan da suka gabata ne aka nemi budurwar aka rasa bayan ta je yi wa wani Owolabi Yusuf girki, wanda babban malami ne kuma saurayinta.
Amma kuma, a rashin sanin dalibar wacce aka saka ranar aurenta da wani mutum daban, Yusuf ya karba Naira miliyan biyu domin ya kasheta don tsafi.
An kama wanda ake zargin a Ilorin ta jihar Kwara bayan 'yan sandan da ke bincike akan batanta sun bibiyi wayarta, sannan suka gano cewa Yusuf ne ya siyar.
A yayin amsa laifinsa, wanda ake zargin wanda ke hannun 'yan sandan yankin Elere da ke Agege, ya ce ya kasheta ne ta hanyar amfani da tabarya da kuma taimakon wasu mutane uku.
Daga nan ne ya yayyankata gunduwa-gunduwa sannan aka yi amfani da ita wurin tsafin, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
KU KARANTA: Hotuna: Yadda ma'aikatan LASEMA suka taimakawa wata mata da bata da gida ta haihu a karkashin gada
KU KARANTA: Yadda wani karamin yaro dan Najeriya ya kera jirgin sama wanda yake tashi
A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga wadanda ba a san ko su waye ba, sun halaka manoma biyu a jihar Nasarawa.
Ana zargin makiyaya ne suka shiga kauyen Icenyam da ke yankin Kadarko Olive a karamar hukumar Keana ta jihar.
Bayanan da aka samu duk da babu yawa a kan harin sun bayyana cewa, 'yan bindigar sun samu manoman a yayin da suke gonakinsu, Vanguard ta wallafa.
Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin. Kamar yadda kakakin rundunar, ASP Rahman Nansel ya sanar a wata tattaunawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya ce tuni rundunar suka tura jami'anta domin tabbatar da zaman lafiya a yankin tare da gujewa mayar da amartani.
Titus Chahur, wanda ya samu zantawa da manema labarai a garin Kadarko, ya yi kira ga gwamnatin jihar da su gaggauta kawo karshe kashe-kashen da suka yi kamari a yankin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng